Sojojin Isra'ila sun harbe Falasdinawa uku a yankin Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu.
"Hukumar kula da al'amuran jama'a ta Falasdinu ce ta sanar da (Ma'aikatar Lafiya) game da shahada da 'yan kasar su uku suka yi ta hanyar harsashin sojojin mamaya a Nablus," a cewar sanarwar da ma'aikatar ta fitar a ranar Talata.
A nasa bangaren, gidan talabijin na Falasdinu ya ce sojojin Isra'ila sun kashe wasu matasa uku.
"Dakarun sojin sun aikata laifin harbin wata mota da ke dauke wasu matasa a cikinta a saman tsaunin Gerizim a Nablus," a cewar gidan talabijin.
Ya kara da cewa an harbi daya daga cikin Falasdinawan ne a wani wuri da ke kusa.
A nasa bangaren, kamfanin dillancin labaran Falasdinu Wafa ya bayyana cewa: "Sojojin mamaya sun hana motocin da ke daukar marasa lafiya hanyar wuce wa, inda suka hana daukar gawarwakin mutanen da suka kashe tare da kwace motarsu.''
Tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye
Isra'ila ta mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan tun bayan yakin kwanaki shida da aka yi a shekarar 1967.
Tun a farkon shekarar da ta gabata ne yankin ke fuskantar samame da dama daga dakarun Isra'ila.