An shirya gudanar da taron Rasha da Afrika a ranakun Alhamis da Juma'a. Hoto: Reuters

Fadar Gwamnatin Rasha ta zargi kasashen Yamma musamman Amurka da yunkurin zagon kasa a taronta na Rasha da Afirka ta hanyar tursasa wa kasashen Afirka kan ka da su halarci taron.

Taron wanda aka shirya gudanar da shi a birnin St Petersburg a ranakun Alhamis da Juma'a, zai samu halartar Shugaba Vladimir Putin wanda ake sa ran zai jagoranci wata tattaunawa kai tsaye mai zurfi da kowane shugaban kasa na kasashen Afirka.

Tattaunawar za ta mayar da hankali kan duk wani abu da ya shafi kasuwanci da tsaro da hada-hadar makamai da kuma batun samar da hatsi.

Taron wanda ake sa ran za a rattaba hannu kan yarjeniyoyi daban-daban, ya biyo bayan babban taron Rasha da Afirka na farko da aka yi a birnin Moscow a shekarar 2019.

Sannan kuma wani bangare ne na bunkasa hadin gwiwar tasirin kasuwanci a nahiyar da sojojin hayar kungiyar Wagner na Rasha ke ci gaba da fafatawa, duk kuwa da kokarin kawar da su da aka yi a gida a karshen wata da ya gabata.

Tawagar kasashen Afirka 49 ne suka ba da tabbaci za su samu halartar taron, kusan rabinsu za su samu wakilcin shugabannin kasashe ko gwamnatocinsu, a cewar jakadan Rasha Alexander Polyakov a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na TASS na kasar ya yi da shi a farkon watan nan.

Batu kan 'yancin kai

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Rasha Dmitry Peskov ya fada a ranar Talata cewa kasashen yamma na iyakacin kokarinsu wajen ganin sun ruguza taron na Rasha.

"Kusan dukkan kasashen Afirka sun fuskanci matsin lamba da ba a taba ganin irinsa ba daga Amurka, haka su ma ofisoshin jakadancin Faransa da ke kasashen ba su yi kasa a gwiwa ba tare da sauran kasashen yammacin duniya wajen kokarin hana wannan taro," a cewar Peskov ga manema labarai.

"A takaice dai, ba su yarda da 'yancin da kasashen Afirka ke da shi ba na tantance abokan huldarsu da kansu domin samun hadin gwiwa da mu'amala da juna a fannoni daban-daban."

Shugaban Amurka Joe Biden ya karbi bakuncin taron Amurka da shugabannin Afirka a birnin Washington a shekarar da ta gabata, inda ya nemi kara karfafa kawancen da ke tsakani a daidai lokacin da dangantakar Rasha da China ke kara karfi a nahiyar.

Tattaunawa kan batun hatsi

Da yake magana a watan Afrilu bayan Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya koka kan yadda kasashen yamma ke kokarin yin zagon kasa ga taron Rasha da Afirka na wannan mako, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce Washington "ba ta son" takaita kawancen Afirka da wasu kasashe. Mu na son bai wa kasashen zabi."

Peskov ya ce taron na Rasha yana da matukar muhimmanci domin zai ba da dama wajen tattaunawa kan batutuwan da suka shafi samar da hatsi da kuma abin da ya kira dabi'ar Moscow na kokarin tallafa wa kasuwannin duniya.

A makon da ya gabata ne Moscow ta sanar da cewa za ta fita daga yarjejeniyar hatsi ta Tekun Bahar Aswad wadda ta bai wa Ukraine - wacce ita da yawancin kasashen yamma suka ce tana yaki da Rasha a kai- kan fitar da hatsi daga tashar jiragen ruwanta, duk da abin da Rasha ta kira "aikin soji na musamman" da take adawa da shi.

Rasha ta yi magana kan yiyuwar samar da hatsi mai araha ko kyauta ga kasashe matalauta na Afirka don maye gurbin hatsin Ukraine tare da cike duk wani gibi da aka samu.

TRT Afrika