Tutar kasar Sudan ke makale a jikin bindigar sojojin Rapid Support Forces (RSF) kafin wani taro da aka yi a kauyen Aprag, mai nisan kilomita 60 daga Khartoum, Sudan, 22 ga Yuni, 2019. / Hoto: Reuters

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta yi watsi da shawarar da kungiyar IGAD ta gabatar ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya domin kawo karshen rikicin kasar.

Hakan na zuwa ne yayin da aka shafe kusan watanni uku ana rikici tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar sa-kai ta Rapid Support Forces (RSF).

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, ma'aikatar ta yi Allah wadai da duk wani yunkuri na girke sojoji a Sudan, tana mai gargadin cewa hakan na iya zama katsalandan a harkokin cikin gida na kasar.

“Bayanin karshe na kungiyar IGAD a taron da ta yi a Addis Ababa ya bukaci a kira taron koli na kungiyar agajin gaggawa ta Gabashin Afirka (EAEF) domin duba yiwuwar tura dakaru da za su kare fararen-hula da samar da hanyoyin shigar da kayayyakin agaji Sudan.

Dangane da haka, gwamnatin Sudan ta tabbatar da cewa taimakon da hukumomin duniya ke bayarwa yana shigowa tare da kai wa ga mabukata, kuma gwamnatin Sudan tana ci gaba da kokarin ganin ta rage wa al'ummarta wahalhalun da suke fama da su, da kuma shawo kan dukkan matsalolin da suke fuskanta a wannan fanni," in ji ma'aikatar.

Kazalika Sudan ta nuna kin amincewarta na "turo ko wace irin rundunar sojin kasashen waje zuwa Sudan kuma za ta dauki hakan a matsayin tayar da zaune tsaye."

Sanarwar ta yi tir da jawaban da shugaban Kenya William Ruto da firaiministan Habasha Abiy Ahmed suka yi a taron kungiyar IGAD inda suka bukaci a tura sojoji da cike gibin da aka samu a fannin tsaro da shugabanci na Sudan.

"Kasancewar tawagar Sudan a Addis Ababa kafin a fara taron da tuntubar wadanda suka shirya taron ta tabbatar da cewa muna son samo hanyoyin warware rikicin da ke ci gaba da wanzuwa a kasar.

Sannan a sanarwar da ake yi a karshen taron na shugabannin kasashen hudu ta rashin halartar wakilanmu ba gaskiya ba ce, in ji ma'aikatar.

TRT World