Sojojin Iran sun kaddamar da sabon jirgin ruwa mai dauke da makami mai linzami

Sojojin Iran sun kaddamar da sabon jirgin ruwa mai dauke da makami mai linzami

Rahotanni sun ce makami mai linzami da ke kan jirgin ruwan na iya tafiyar kilomita 600.
An shafe shekaru ana samun rashin jituwa tsakanin Amurka da Iran. Hoto/Reuters

Sojojin juyin juya hali na ruwa na Iran sun kaddamar da wani sabon jirgin ruwa dauke da makami mai linzami mai dogon zango. Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ce sabon makamin yana tafiya mai nisan kilomita 600.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Iran din ke ci gaba da zaman doya da manja da Amurka.

Duk da cewa kamfanin dillancin labaran na Tasnim bai bayar da cikakken bayani kan jirgin ruwan da makamin ba, amma ya ce an sanar da kaddamar da jirigin a lokacin da wani atisayen soja a gabar Tsibirin Abu Musa, wanda yana daya daga cikin tsibirai uku na yankin Gulf da ke karkashin ikon Iran amma Hadaddiyar Daular Larabawa ke takaddama a kai.

Sai dai kamfanin dillancin labaran ya ruwaito wani kwamanda yana cewa akwai bukatar a kare wannan tsibirin.

“Tsibiran da ke Tekun Pasha na daga cikin martabobin da Iran ke da su kuma za mu kare su,” in ji kwamandan sojojin ruwa na rundunar juyin juya hali ta Iran Alireza Tangsiri, inda ya kara da cewa akwai bukatar kasashen da ke yankin su samar da isashen tsaro.

“Tekun Pasha na duka kasashen yankin ne... Dole ne wadannan kasashen su bi a hankali da kuma kiyaye kansu daga fadawa cikin makirci da kuma sharrin raba kai daga wasu kasashe na wasu yankuna,” kamar yadda ya kara da cewa.

A watan da ya gabata, Amurka ta tura karin jiragen yaki nau’in F-35 da F-16 da kuma jiragen ruwa na yaki zuwa Gabas ta Tsakiya, duk a yunkurin kasar na samun gindin zama a yankin bayan da Iran ta kwace wani jirgin jigilar kayayyaki a watannin baya.

TRT Afrika da abokan hulda