Arewa maso-gabashin Indiya na sauya wa zuwa matattarar rikicin Kiristoci da mabiya Hindu

Arewa maso-gabashin Indiya na sauya wa zuwa matattarar rikicin Kiristoci da mabiya Hindu

Manipur ne cibiyar gwagwarmaya tsakanin kabilu Kiristoci da kuma al'ummu mafiya rinjaye da ke bin addinin Hindu.
Indiya na fama da rikice-rikicen kabilanci da addini. Photo: AFP

A farkon watan Mayu rikicin kabilanci da addini a Jihar Manipur da ke arewa maso-gabashin Indiya ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da 100, mafi yawansu farar hula.

Rikici ya yi tsami tsakanin ‘yan kabilar kuki, da mafi yawancin su Kiristoci ne, da kuma ‘yan kabilar Meitei mafiya rinjaye da ke bin addinin Hindu.

Rikicin da ya tsugunar da dubban iyalai, tare da lalata gidaje da wuraren kasuwanci, ya janyo zaman dar-dar a tsakanin al'ummun, kuma ya kawo tambayar ko gwamnatn Indiya ta shirya daukar wani mataki game da lamarin.

Rikicin kabilanci ne ya rarraba kawunan jama’a a Manipur, daya daga cikin jihohin Indiya bakwai a yankin arewa maso-gabas, in ji Ministan Harkokin Cikin Gida Amit Shah.

Manipur yanki ne da ya tattara kabilu daban-daban, da suka hada da al’ummar Kuki, wadanda suke zaune a jihar mafi nisa a Indiya.

Al’ummar Kuki na warwatse a kauyuka da ke kan tsaunukan Manipur.

Dokokin Indiya sun ba su wani matsayi na musamman, inda ake musu alfarmomi kamar guraben ayyukan gwamnati da kuma mallakar kadarori.

Rikicin ya samo asali ne bayan wata shawara da aka yanke don bai wa jama’ar Meitei irin wancan matsayi na alfarma, da zai ba su damar mallakar kasa, samun tallafin tattalin arziki, ayyuka da tallafin ilimi.

Babbar Kotun Manipur ta bukaci Jam’iyyar Bharatiya Janata ta ‘yan kishin kasa da gwamnatin Jihar Manipur ke jagoranta, da ta biya bukatar jama’ar Meitei.

Duk da cewar wannan umarni na kotu ya ingiza afkuwar rikicin, wasu batutuwa da suka shafi abubuwan da Babban Minista N. Biren Singh ya yi ne suka ta’azzara wannan fada.

Matsala ce daga waje?

Akwai rabuwar kan jama’a a Manipur, wajen da al’ummu daban-daban ke rayuwa.

Jama’ar kabilar Kuki da sauran kabilu na rayuwa a gidajen da ke kan duwatsu kuma a dazuka.

A daya bagaren kuma, al’ummar Meitei da suke da yawan sama da kaso hamsin na jama’ar Manipur, na rayuwa a birane da ke cikin wadi, da ke ciki da wajen babban birnin Imphal.

Amma kuma wadin Imphal na da girman kaso 10 na kasar yankin ne, kuma Meitei ba su da ‘yancin sayen filaye a yankunan da ke da kabilu, amma kuma sauran kabilu na da ‘yancin sayen filayen a yankunan da Meitei suke rayuwa.

Wannan ne ya sanya jama’ar Meitei suka nemi cewa su ma a ba su ‘yanci – ko da hakan zai kai ga saka su a jerin kabilu na musamman.

Haka zalika, matsin lamba na daduwa game da karuwar jama’a a Manipur sakamakon yadda ‘yan gudun hijira daga Myammar mai makotaka da kasar ke zuwa bayan gujewa rikicin kasarsu.

Kusan kaso 1 cikin 4 na iyakar Myammar da Indiya da ke da nisan kilomita 1600 ta gifta ne ta Manipur da manyan yankunan Myammar guda biyu, Yankin Sagaing – zuwa gabashin Manipur da kuma jihar Chin – da ke bangaren kudu.

Kwararowar ‘yan gudun hijirar ya janyo damuwa ga gwamnatin Manipur inda ake samun gine-gine da ba sa bisa ka’ida a tsaunukan da ke kan iyaka na karuwa sosai tun bayan da rikicin Myammar ya tsananta a shekarar 2021.

Gwamnatin Indiya ba ta yi wani katabus ba don magane kwararowar ‘yan gudun hijirar.

Da yawa daga ‘yan gudun hijirar da ke zuwa daga Myammar na da alakar kabila da wasu jama’ar Manipur.

Meitei na bayyana tsoron idan adadin ‘yan gudun hijirar Myammar ya ci gaba da karuwa a yankin, to za a fi su yawa.

Matsala da ke kurkusa da gida

A lokacin da babu wata shaida da za ta danganta gwamnatin Indiya da wannan rikici, Shugaban Manipur, Singh ya kara ta’azzara lamarin tun bayan hawa mulki a 2022 a karo na biyu a jere.

Akwai wadanda ke bayyana cewa tabbas shugaban na jam’iyyar BJP na goyon bayan ‘yan kabilarsa, Meitei mafiya rinjaye da ke bin addinin Hindu, don ganin sun danne sauran kabilun yankin.

Misali, an soki Singh bayan da ayyana wasu jama’ar Kuki a matsayin ‘yan ta’adda. Irin wadannan kamalai za su zama bala’i ga jihar da ta jima tana fama da rikicin addini da kabilanci.

Ba wannan ne kadai misalin irin wadannan kalaman nuna wariya da rashin kan gado ba.

Shugaban ya kuma alakanta kwararar ‘yan gudun hijira daga Myammar zuwa kasar da kabilun wajen, inda yake mai amfani da fiffa da launi a shafukan sada zumunta.

A wani sakon Tuwita da ya fitar, wanda ya goge daga baya, Singh ya kira jama’ar Kuki da ‘Banzaye’ a lokacin da yake zargi mara tushe kan cewar Kiristoci sun lalata Manipur ta hanyar aikata muggan laifuka kamar safarar miyagun kwayoyi, noman wiwi da satar dukiyoyin jama’a.

Irin wadannan kalamai na rashin kan gado ne ya sanya wasu ‘yan jam’yyarsa ke kiran sa “Makiyin Kuki”.

Jama’ar Kuki sun ki zama a teburin sulhu da gwamnatin New Delhi ta kafa saboda Singh na daga cikin mambobin kwamitin.

Singh ya sha fitar da sanarwar nuna kiyayya ga Kuki tun kafin rikicin baya-bayan nan ya afku.

A Manipur da ake da adadin Kiristoci da mabiya addinin Hindu da yawa, kalaman tunzura da nuna kiyayya daga shugaban jiha ne suke zama tushen ruruwar rikicin.

A mafi yawan yankunan, kabilu na bautar dabbobi, shamanism da addinin Kirista.

Hare-hare kan jama’ar Kuki na zuwa ne a matsayin kokarin kakaba musu karbar manufar kishin kasa ta jama’ar Hindu, wadda ta samo asali daga akidar Rashtriya Swayamsevak Sangh da suke da rikici.

Tsawon shekaru, masu rajin akidar Hindutva ta RSS sun dinga kokarin sauya tunanin sauran kabilun arewa maso-gabashin Indiya kan su karbi wannan akida ta Hindu.

A littafinsa “The Greater Experiment”, marubuci kuma mai bincike Arkotong Longkumer ya rubuta cewa “Karo na farko da na hadu da jama’ar Hindu nigari shi ne lokacin ina binciken karatun digirgir a tsakanin 2004-2005 a Haflond da Laisong a gundumar Dima Hasao da ke jihar Assam (Babbar jiha a arewa maso-gabashin Indiya).

"Na kadu da yadda na ga suna jajircewa wajen koyarwa a makarantun kauyuka da ke karkashin kulawar Vishwa Hindu Parishad.

"Mu’amalata da su ta sanya na fahimci burinsu na isar da ayyukansu ga dukkan yankin. A tsawon lokaci, ina ganin yadda wannan buri nasu ke mamaye yankin sannu a hankali.”

RSS na da imanin cewa za su iya zama wata kungiyar addini kamar masu bautar dabbobi da Shamanism don yakar yaduwar addinin Kirista – wanda ya zi Manipur da kewayensa a karni na 17.

Masu kishin kasa daga al’ummar Hindu na kuma aikata wasu abubuwa da ke dakile jama’ar karkara.

Misali, wata jihar arewa maso-gabas ta Arunachal Pradesh, masu yada addinin Hindu na yin wa’azi da cewa ‘Donyi-Polo’ rana da wata daidai suke da addinin Hindu.

Amma rikicin da ake yi ya amfani reshen siyasa na RSS, - BJP ta tsinci kanta a gwamnati a jihohi shida daga bakwai na yankin - amma kuma sun bige a rikicin kabilanci.

Manufar Hindutva ta yin kudin goro ga mabiya addinan gargajiya da Hindu a matsayin abu daya ya janyo hare-hare kan coci-coci da ke yankin.

A Manipur wata kungiya da ke da coci mai sunan ‘Goodwill Mission’ – ta bayyana cewa an lalata cocina ko wuraren bautar Kiristoci kusan 300 a rikicin karshe da aka yi.

An kuma lalata wasu wuraren bautar Hindu, wanda hakan ya sanya aka kasa shawo kan lamarin.

Rikicin Manipur na bayar da wani haske na gazawar gwamnati.

Makonnin da suka gabata an fasa ma’ajiyar makaman ‘yan sanda tare da sace makaman, wanda ya ta’azzara rikicin.

Kungiyoyi dauke da makamai, wanda a baya suka lafa kuma suke a dukkan al’ummun, sun taimaka wajen girmamar rikicin.

Ya zama dole gwamnatocin BJP a New Delhi da Manipur su dauki matakin gaggawa kafin al’amarin ya gagari kundila.

Wani bangare na kungiyoyin farar hula a Indiya ya bayar da shawarar a kafa wani kwamitin shari’a irin na Afirka da zai dauki bangare ba, a cikin gida don dawo da zaman lafiya a yankunan da ake fama da rikicin.

A 1996 Afirka ta kudu ta kafa kwamitin dawo da adalci – Kwamitin Gaskiya da Sulhu – da manufar sasanta kabilun da ke rikici da juna don tabbatar da zaman lafiya.

A 1999 an sake kafa irin wannan kwamiti mai suna Kwamitin Hadin Kann Kasa da Sulhu a Rwanda. Duk sun samu nasara.

Tabbas gwamnatin Indiya ta kafa kwamitin zaman lafiya karkashin gwamnan Manipur da ya dauki bangaranci, amma a ranar 11 ga Yuni, jama’ar Kuki sun kauracewa kwamitin.

Sun ce saka shugaban yankin Singh ne ya sanya ba za su halarta ba wanda hakan ya sabawa manufar ganawar, hakan na nufin idan ba a samar da tsari na adalci ga kowanne bangare ba.

A ranar 14 ga Yuni sabon rikici ya balle, wanda ya shaida akalla mutuwar mutum tara, wanda hakan ya gurgunta duk wani aiki na neman a zauna lafiya a yankin.

TRT World