Gomman 'yan majalisar dokokin Amurka na Jam'iyyar Democrat mai mulki sun nemi Shugaba Joe Biden ya bijiro da batun take hakkin dan adam a tattaunawar da zai yi da Firaiminsitan Indiya Narendra Modi yayin ziyararsa a Washington a wannan makon, a wata wasika da suka aike wa shugaban.
Modi ya isa Amurka a ranar Talata a wata ziyara da ake gani a matsayin ta karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
'Yan majalisar dokokin Amurkan sun ce sun damu kan yadda ake musguna wa mutane saboda bambancin addini da hana 'yancin fadin albarkacin baki da hana damar amfani da intanet da kuma kai wa kungiyoyin fararen-hula hari.
"Ba mu ba da shawarar a zabi kowane shugaba ko jam'iyya ba a Indiya — wannan zabin da Indiyawa suka yi wa kansu ne — amma ba ma goyon bayan duk wasu muhimman akidu da suke kan gaba a cikin muradun Amurka na kasashen waje," kamar yadda wasikar ta kunsa, wacce Sanata Chris Van Hollen da 'yar majalisar wakilai Pramila Jayapal suka jagoranci rubutawa.
Sanatoci da 'yan majalisar wakilai 75 na Jam'iyyar Democrat ne suka sanya hannu kan wasikar, wacce aka aike ta zuwa Fadar White House a ranar Talata, inda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fara ruwaito batun.
"Kuma muna so, a yayin ganawarka da Firaiminista Modi, ku tattauna batutuwa masu muhimmanci don a samu zarafin karfafa dangantaka mai tsawo tsakanin kasashen biyu," in ji wasikar.
Sau biyar Modi na ziyartar Amurka tun bayan zamansa firaiminista a shekarar 2014, amma wannan ne karo na farko da zai je a matsayin cikakkiyar ziyarar diflomasiyya, duk da irin damuwar da ake nunawa kan yadda batun hakkin dan adam ke tabarbarewa a karkashin mulkin jam'iyyarsa ta Bharatiya Janata Party [BJP].
Washington na fatan a karfafa dangantaka tsakaninta da kasar da ta fi girman dimokuradiyya, wacce take ganin tana wuce China, amma damuwar da ake da ita kan batun hakkin dan adam na dusashe komai.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam da dama sun shirya yin zanga-zanga a yayin ziyarar ta Modi.
Rahoton shekara-shekara na Ma'aikatar Tsaron Amurka da aka sake a watan Maris ya lissafa "manyan batutuwan take hakkin dan adam da ake yi a Indiya."
Gwamnatin Indiya karkashin jagorancin Jam'iyyar BJP tana goyon bayan wariyar da ake nunawa mabiya addinai tsiraru a matakin jihohi da na tarayya, kuma Hukumar Kula da 'Yancin Addini ta Amurka USCIRF ma ta yi kira ga Shugaba Biden da ya bijiro wa da Modi wadannan zantuka.
"Akwai matukar damuwa ganin yadda gwamnatin Indiya ke ci gaba da sanya tsare-tsaren da suke yin mummunan tasiri a kan Kiristoci da Musulmai da mabiya addinin Sikh," in ji shugaban hukumar USCIRF, Stephen Schneck.