Hoton shanu irin Nelore a wajen kiwo / Hoto: Getty

Saniya nau'in Nelore’ - wacce ta samo asali daga Indiya – ta zama dabba mafi tsada a duniya bayan an yi gwanjonta kwanan baya a kan dala miliyan 4.3.

Saniyar, mai shekara hudu da rabi da ake kiranta da suna Viatina-19 FIV Mara Emovis, a yanzu haka ta zama shahararriya a kasarta bayan gwanjonta da aka yi, inda yankin Agropecuaria Casa Branca ta sayar da wani bangaren jikinta ga Nelore HRO a kan dala miliyan 1.44.

Saboda tsadarsu, kamfanoni ko daidaikun mutane ke hada hannu don mallakar nau’in shanun Nelore.

A taron gwanjon da aka yi a yankin Arandu da ke jihar Sao Paulo, kashi uku na kudin da aka samu ya kai fam din Brazil miliyan 6.99 (dala miliyan 1.44).

A bara, an sayar wa rabin wadanda suka mallaki saniyar a taron gwanjonta da aka yi a Brazil a kan dala 800,000.

Kudaden da aka samu sun nuna bukatar da ake da ita daga Brazil wajen samar da ingantattun nau’in shanun wadanda aka ce suna hayayyafa da sauri idan aka yi barbarar nau’in saniyar Nelore da wani nau’in na daban.

Saniya nau’in Nilore na iya jure wa yanayin zafi fiye da sauran nau’ukan shanu da ake da su a kasar, abin da ake ganin ya dace da wasu wuraren kiwo marasa inganci a Brazil.

Taurin fatar da saniyar ke da shi yana sa nau'inta yana iya juriya ga cizon kwari da sauransu.

Adadin kudin da aka sayar da saniyar a kwanan baya a cewar Jaridar Newsweek ya nuna yadda dabbar, mai launin farin jiki, ke da inganci da kuma yadda take iya jure ko wanne irin yanayi da kasar kiwo.

Farin gashin da ya lullube jikinta na taka muhimmiyar rawa, inda yake bayyana haske mai yawa, yayin da sassan da ke fitar da gumi na jikin dabbar ya ninka girmansa, sannan kusan kashi uku fiye da nau'in shanu na Turai.

Saniyar Nelore ta fito ne daga dangin Bos Indicus, tana da babban tozo a kafadunta. Ana kuma kallonta a matsayin nau'in kiwo mai kyau, inda jinsin matanta suke da faffadan kugu da ke bude da kuma babbar mahaifa fiye da sauran dangin shanu da ake da su.

Bincike ya yi nuna da cewa nau'in jinsin na iya haihuwa da yawa da kuma yaye idan aka kwatanta da sauran shanu.

Kasar Brazil ce ta fi ko wacce kasa nau’in saniyar Nelore, inda ake fitar da ita zuwa wasu yankuna a fadin Amurka da kuma kasashen Argentina da Paraguay da Venezuela da Mexico a cewar kungiyar kiwo shanu ta Cattlesite.

Rahotanni sun nuna cewa akwai kimanin shanu miliyan 167 a Brazil, wanda ke wakiltar kusan kashi 80 cikin 100 na yawan shanun yankin.

Sayar da maniyyin nau’in saniyar Nelore na wakiltar kashi 65 cikin 100 na kasuwar Barbara na kowane nau'i dabba a Brazil, inda masana'antar ke dada bunkasa tun shekarun 1960, a cewar Jami'ar Jihar Oklahoma.

Asalin tarihin shanun ya biyo fiye da shekaru 2000 da suka wuce, lokacin da aka ce an shigo da su Indiya, inda a yanzu haka shanun ke da matukar mahimmanci ga addinin Hindu.

A tarihin irin nau'in, ya fuskanci yanayi mai tsanani kama daga rani da sanyi da kuma yanayin zafi a Indiya.

Kungiyar Cattlesite ta ce Ongoles, wani irin nau'in Nelore ne, da aka gano shi a Brazil a shekarar 1868 lokacin da wani jirgin ruwa da ke kan hanyarsa ta zuwa Birtaniya ya tsaya a Salvador da Brazil, inda aka sayar da shanun.

Shekaru da dama da suka wuce, wani mai kiwo daga Rio de Janeiro ya sayi wasu ma'aurata daga gidan namun daji na Hamburg da ke Jamus, inda sannu a hankali nau’in jinsin ya kara fadada sawunsa a fadin Brazil daga Bahia da Mina Gerais da kuma Uberaba.

TRT World