Masu zanga-zangar sun yi arangama da 'yan sanda bayan mutuwar Nahel, wani matashi dan shekara 17 da wani dan sandan Faransa ya harbe. / Hoto: Reuters

Mutane 667 ne aka kama cikin dare a Faransa, a cewar Ministan harkokin cikin gida Gerald Darmanin, bayan zanga-zangar da ta barke a dare na uku a jere a fadin kasar, sakamakon harbin wani matashi da 'yan sanda suka yi a farkon mako.

Hukumomin kasar na hasashen barkewar zanga-zangar har nan da kwanaki masu zuwa sakamakon mummunan harbin da aka yi wa matashin, yayin da a bangare guda suke kokarin shawo kan rikicin da ke dada ta’azzara inda aka dakatar da zirga-zirgar ababen hawa tare da sanya dokar hana fita.

A wata takardar bayanin tsaron cikin gida da aka fitar, ana sa ran a lokutan "dare masu zuwa" za a fuskanci tashin hankali tare da barnata wasu kayayyaki a birnin inda za a fi mai da hankali kan jami’an tsaro da wasu muhimman alamomi a birnin", a cewar wata majiya ta 'yan sanda a yammacin ranar Alhamis.

Tuni dai aka ayyana dokar hana fita da daddare a unguwar Clamart da ke Paris, tsakanin karfe 9:00 na dare [1900 GMT] zuwa 6:00 na safe daga ranar Alhamis har zuwa Litinin mai zuwa.

A wani mataki na bayyana irin tashin hankali da aka shiga, an gudanar da tattakin don tunawa da Nahel M. dan kimanin shekaru 17 da 'yan sandan suka kashe.

Bayan haka ne rikici ya barke inda ‘yan sanda suka yi ta harba barkonon tsohuwa yayin da aka kona motoci da dama a unguwar da aka kashe matashin.

Faransa na fama da zanga-zanga bayan harbe Nahel, wanda aka nada a bidiyo lamarin da ya fusata al’umma tare da tafka muharawa kan aikin 'yan sanda

"Dole ne duniya ta ga cewa mun yi tattaki kan abin da aka yi wa Nahel," in ji dan gwagwarmaya Assa Traore, wanda dan uwansa ya mutu bayan an kama shi a shekarar 2016.

Dubban 'yan sanda ne suka bazu a kan tituna

An tuhumi dan sandan da ake zargi da harbin Nahel a Nanterre da laifin kisan kai da son rai, kuma yana tsare a gidan yari, sai dai ana jira a ga irin tasirin da hakan zai iya haifar da tarzoma da ta barke.

An baza 'yan sanda kusan 40,000 don kokarin samar da zaman lafiya a ranar Alhamis, fiye da adadin da ke kasa a ranar Laraba, inda aka kama mutane da dama.

An kona motoci da tantuna a daren Alhamis a wasu sassan kasar, yayin da aka kama mutane 150 a fadin kasar bayan barkewar rikicin da ya haifar da kona motocin dakon kaya a wata unguwa da ke birnin Paris.

Za a dakatar da ayyukan bas-bas na Paris da na kananan jirgin kasa bayan karfe 9:00 na dare (1900 GMT) ranar Alhamis, a cewar shugaban yankin.

Shugaba Emmanuel Macron ya yi kira da a kwantar da hankula kuma ya ce tashin hankalin da aka yi a zanga-zangar "bai dace ba".

Rikicin dai ya yi matukar damun Macron wanda ke kokarin farfadowa daga mumnunar zanga-zangar da aka kwashe tsawon lokaci ana yi kan garambawul din tsarin fansho da ya yi a kasar.

'Harsashi a kai'

An kashe matashin ne a lokacin da yake kokarin guje wa ‘yan sandan da suka yi yunkurin tsayar da shi saboda ya saba wa ka’idojin bin hanya.

Wani bidiyo da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tabbatar da sahihancinsa, ya nuna yadda wasu ‘yan sanda biyu ke tsaye a gefen wata mota suna nuna wa direban cikinta makami.

An nadi wata murya tana cewa: "Za mu harbe ka da harsashi a kai."

Daga nan sai dan sandan ya yi yunkurin harbi a daidai lokaci da motar ta tashi da sauri.

Tashin hankalin ya barke ne bayan bayyanar bidiyon, da ya saba bayanan da ‘yan sanda suka fitar kan cewa matashin ya yi kokarin bin ta kan tuki dan sandan ne.

A daren ranar Alhamis, zanga-zanga ta bazu zuwa birannen Toulouse da Dijon da Lyon da wasu garuruwa da dama a yankin Paris.

A ranar Laraba da Alhamis, masu zanga-zangar sanye da bakaken kaya sun banka wuta a wurin da aka kashe Nahel M.

Hayaki mai kauri ya turnuke saman wurin da aka cinnawa motoci goma sha biyu da kwandon shara wuta tare da toshe shingayen ababen hawa.

A birnin Paris, 'yan sanda sun harba kwalabe don tarwatsa masu zanga-zangar da suka mayar da martani su ma.

A birnin Toulouse da ke kudancin kasar, an kona motoci da dama tare da jifan 'yan sanda da jami'an kashe gobara da harsasai.

Magajin garin ya shaida wa kamfanin dillancin labarean AFP cewa, an kona dakin taron garin Mons-en-Baroeul da ke wajen birnin Lille da ke arewacin kasar, a lokacin da wasu mutane 50 da suka hade kansu tare da kutsa kai cikin ginin.

Firayim Minista Elisabeth Borne, wacce ta yi magana a wani gari da ke arewacin Paris inda aka kona ofishin magajin gari, ta ce " dole ne a yi kokarin kaucewa duk wata hayaniya ".

'Abubuwan da ke haifar da tashe-tashen hakula'

Faransa ta yi fama da matsalar barkewar tarzoma a shekarar 2005, sakamakon mutuwar wasu yara maza biyu ‘yan asalin Afirka, a wani harin da ‘yan sanda suka kai, inda aka kama mutane 6,000.

"Akwai abubuwa da dama da za a yi la’akari da su wadanda ke iya haifar da barkewar tarzoma a kasar," kamar yadda wani mai ba gwamnati shawara ya shaida wa AFP.

Shugaban 'yan jam'iyyar Republican na dama, Eric Ciotti, ya yi kira da a kafa dokar ta-baci, wadda za ta bai wa kananan hukumomi damar samar da wuraren da ba a zuwa, sai dai wata majiya ta gwamnati ta shaida wa AFP cewa a halin da ake ciki babu wannan zabin a kasa.

Ana ci gaba da nuna damuwa kan dabarun da ‘yan sanda ke amfani da, musamman kan samari tsiraru da ba fararen fata ba.

A bara, an kashe mutane 13 bayan da suka ki tsayawa domin binciken ababen hawa da ‘yan sanda ke yi, bayan nan ne aka sauya doka a shekarar 2017 da ta bai wa jami’an karin karfin yin amfani da makamansu.

"Abin da nake gani a wannan bidiyon shi ne hukuncin kisa da 'yan sanda suka yi wa wani yaro dan shekara 17, a Faransa, a shekarar 2023, da rana tsaka," in ji shugabar jam'iyyar Greens Marine Tondelier.

TRT World