‘Yan sandan Faransa sun kama karin akalla mutum 719 a daidai lokacin da ake mummunar zanga-zanga a kasar wadda ta samo asali bayan wani dan sanda ya kashe wani matashi a kasar.
Akalla ‘yan sanda 45 da kuma jandarmomi aka raunata haka kuma akalla mutum 719 aka kama a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a ranar Asabar da dare, kamar yadda ministan harkokin cikin gida na kasar ya tabbatar.
Kusan mutum 2,700 aka kama tun bayan soma wannan zanga-zanga.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Faransar ta kara da cewa akwai ‘yan sanda da jandarmomi 45,000 da aka jibge da kuma dubban masu kashe gobara a tsawon daren na Asabar.
A ranar Lahadi, ministan cikin gida Gerald Darmanin ya wallafa wani sako a shafin Twitter inda ya yi godiya ga ‘yan sandan kasar sakamakon saukin da aka samu na zanga-zangar a cikin dare.
Abin da ya jawo zanga-zangar
Zanga-zangar wadda aka soma bayan kashe Nahel M. wanda matashi ne mai shekara 17 wanda dan asalin Aljeriya ne, na ci gaba da girgiza Faransa.
Dan sandan ya saita Nahel inda ya yi masa harbi na kusa da kusa a birnin Paris a ranar Talata.
Dan sandan na fuskantar tuhuma kan kisa dagangan inda aka tsare shi na wucin gadi.