Kasuwancin shinkafar yankin Asiya ya tsaya cik bayan dokar hana fita da shikafa da kasar Indiya wacce ke zama kasa mafi girma da ke samar da ita a duniya ta sanya a baya-bayan nan kan wani kaso mai yawa na kayayyakin da take fitar wa zuwa kasashen waje.
An yi hasashen farashin shinkafa a kasar zai yi tashin gwauron zabi a ‘yan kwanaki masu zuwa, a cewar wasu ‘yan kasuwa uku.
Indiya, wacce ke da kashi 40 cikin 100 na shinkafar da ake fitarwa a duniya, a ranar Alhamis ta ba da umarnin dakatar da fitar da mafi yawan shinkafar da take fitarwa, don rage farashin cikin gida da ya fuskanci tashin gwauron zabi a 'yan makonnin nan sakamakon rashin kyawun yanayi da ke barazana ga ayyukan noma.
"Farashin shinkafa zai karu a kasuwannin fitar da kayayyaki, muna dai sa ran samun mafi karancin ribar da za samu ta kai dala 50 a kan kowane tan, ko ya kai dala 100 ko ma fiye," in ji wani dan kasuwa a Singapore a wani kamfanin kasuwanci na kasa da kasa.
"A halin yanzu, kowa - masu sayarwa da masu saye - suna jiran ganin yadda kasuwar za ta tashi," in ji dan kasuwar.
"Ba mu ji labarin wani ciniki da aka yi a yau ba amma masu saye za su biya farashi mai yawa don samun kaya saboda matakin da Indiya ta dauka ya sanya an fitar da adadi mai yawa daga kasuwa," a cewar wani dan kasuwar Singapore na daban.
Matakin da Indiya ta dauka na hana fitar da shinkafa zuwa kasashen waje ya zo a daidai da ci gaban da aka samu a kasuwannin alkama na duniya wanda ya haifar da fargabar hauhawar farashin kayan abinci.
Noman shinkafa na fuskatar hadari sakamokon yanayin zafi na El Nino
Farashin alkama a duniya ya haura sama da kashi 10 cikin 100 a wannan makon, adadin shi ne mafi girma a ribar mako-mako da aka samu a sama da watanni 16, yayin da hare-haren da Rasha ke kai wa tashoshin jiragen ruwa na Ukraine ke kara haifar da damuwa kan wadatar da duniya za ta samu na alkkama.
Shinkafa ita ce nau’in abinci da mutum fiye da biliyan uku suka fi ci, sannan ana noma kusan kashi 90 cikin 100 na amfanin gona da ke bukatar ruwa a yankin Asiya, inda a yanzu yanayin zafi na El Nino ke barazana ga samunta.
A yanzu haka a Thailand, wacce ita ce kasa ta biyu mafi girma a duniya da ke fitar da shinkafa zuwa kasashen ‘yan kasuwa na jira don tabbatar da farashin kayan kafin su sanya hannu kan sabbin yarjejeniyoyi.
"Masu fitar da kayayyaki ba za su so su sayar ba, don ba su san ainihin farashin da za su bayar ba," a hirar da kamfanin dillanci labarai na Reuters ya yi da Chookiat Ophaswongse, shugabar karramawar kungiyar masu fitar da shinkafa ta Thai.
"Wasu 'yan kasuwa suna tsammanin farashin zai iya kai wa dala 700 zuwa 800 a kan kowane tan.
Farashin shinkafa a manyan kasuwanin kasashe da ake fitar da kayayyakin ya yi tashin gwauron zabi saboda matakin da Indiya ta dauka na hana fita da kayayyakin.