Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na Turkiyya Sedat Onal ya bayyana muhimmancin bin matakan kare hakkin Azarbaijan da kuma irin kokarin da Turkiyya ke yi wajen cimma hakan da Armeniya a karshen taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. /Hoto: AA

Turkiyya na ci gaba da goyon bayan tattaunawar zaman lafiya tsakanin Azabaijan da Armeniya, a cewar Jakadan Turkiyya na Majalisar Dinkin Duniya Sedat Onal.

Sedat ya bayyana haka ne a yayin wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan tattauna halin da ake ciki a Karabakh bisa bukatar Yerevan.

"A matsayinta na kasar da ke da muradin ganin yankuna sun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma himma wajen aiwatar da wannan manufa, Turkiyya ta damu matuka da yunkurin Armeniya na amfani da damar da ta samu daga kasashen waje, ciki har da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, don bayyana zarge-zargenta na siyasa da suka dauki hankali kan hanyar Lachin," cewar Sedat Onal yayin taron kwamitin tsaron a ranar Laraba.

Ya kara da cewa akwai bukatar a tunkari lamarin ta "hanyar da ta dace," yana mai cewa dole ne a yi la'akari da halin kuncin da Azarbaijan ke ciki.

"Azabaijan ta dade tana nuna damuwarta kan yadda ake amfani da hanyar Lachin wajen samar da makamai ga kungiyoyin ta’addanci tare da hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Karabakh,’’ in ji shi.

A cewarsa, "ganin ba a mai da hanakali kan wadannan korafe-karafen ba, Azerbaijan ta ga ya zama wajibi ta dauki matakai kan yankinta yadda ta ga ya dace cikin tsarin 'yancinta."

Jakadan na Turkiyya ya ce ana iya bi da kayayyaki irin su magunguna ta hanyar Lachin, kazalika Azabaijan ta ware hanyar Aghdam-Khankendi don kai abubuwan bukatu ga al'ummar Armeniya a Karabakh.

"Duk da haka, Azarbaijan ta bayyana shirinta na tattaunawa da wakilan al'ummar Armeniya don magance matsalar ta hanyar da ta dace. Amma abin takaicin shi ne, ba a jinjina mata bisa kyakkyawar aniyarta da kokarinta ba," in ji shi.

A jawabin wakilin Azerbaijan na Majalisar Dinkin Duniya, Yashar Aliyev a taron na kwamitin sulhun MDD, ya bayyana zarge-zarge Armeniya game da toshe hanyar Lachin a matsayin batu da ‘’ba shi da tushe balle makama.’’

Ya kara da cewa, "Ayyukan da Armeniya ke yi ba wani abu ba ne illa wani tsari na munafunci na siyasa da aka tsara, kuma kiran da ta yi wa kwamitin sulhu na daga cikin kamfen din da ta shafe tsawon watanni tana yi na yin magudi da kuma gusar da hankalin kasashen duniya."

Ministan harkokin wajen kasar Armeniya Ararat Mirzoyan ya ce ya je kwamitin sulhun ne domin neman goyon bayansu wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, yana mai zargin Azarbaijan da "mummunan tashin hankali na jinkai" a Karabakh.

Armeniya ta yi ikirarin cewa Azerbaijan ce ta rufe hanyar Lachin, zargin da birnin Baku ya yi watsi da shi.

TRT World