Azerbaijan na gudanar da wani taro kan ''manufofin Faransa na sabon salon mulkin mallaka a nahiyar Afirka'' inda masu jawabai suka dinga sukar Faransa da kakkausar murya a kan yadda take ci gaba da tsoma baki cikin al'amuran ƙasashen da suka yi wa mulkin mallaka a baya.
Taron na ranar Alhamis ya zo ne a daidai lokacin da kasashen Afirka da dama ke ci gaba da samun ƙaruwar kiraye-kirayen neman 'yancin kai, musamman ma dangane da dangantakarsu da Faransa da wasu Ƙasashen Yammacin Duniya.
Kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali sun kawo karshen huldar soji da ƙasar, a shekarun baya-bayan nan, wadda ta mulke su a baya.
Wata kungiya mai zaman kanta ta Baku Initiative Group (BIG) ce ta shirya taron a Baku, babban birnin kasar Azabaijan.
A yayin jawabin bude taron, Abbas Abbasov, babban daraktan kungiyar, ya nuna cewa tasirin Faransa a Afirka ya wuce kasashen da ta yi wa mulkin mallaka kuma ba za a iya kawar da ita ba tare da kawo cikas ga tsarin zamantakewar da ake ciki ba.
Masu jawabai sun yi kira da a kara samun ‘yancin cin gashin kai na tattalin arziki daga Faransa, musamman kan kudin CFA, da kuma tsaron yankin.
An kuma karfafa gwiwar gwamnatocin kasashen Afirka da su bi kiran da aka yi na sake tattaunawa kan batun binciken albarkatun kasa da kamfanonin Faransa ke yi don kara musu amfani ga tattalin arzikinsu.