Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya nemi afuwar takwaransa na Azabaijan kan abin da ya kira "mummunan al'amari" da ya faru biyo bayan hadarin da jirgin saman Azabaijan ya yi a Kazakhstan wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 38.
A cikin wata sanarwa a hukumance a ranar Asabar, Fadar Kremlin ta ce na'urorin tsaron sararin samaniya sun yi luguden wuta a kusa da Grozny a ranar Laraba saboda wani harin da jirgin saman Ukraine maras matuƙi ya kai, amma shugaban bai bayyana ko na'urorin tsaron ne suka harbo jirgin ba.
A ranar Juma'a, wani jami'in Amurka da wani ministan Azerbaijan sun fitar da sanarwa daban-daban inda suka ɗora alhakin faduwar jirgin a kan wani makami daga waje.
A ranar Laraba ne jirgin ya tashi daga Baku babban birnin kasar Azerbaijan zuwa Grozny babban birnin yankin Jamhuriyar Chechnya wanda ya sai ya samu hatsari a lokacin da yake ƙoƙarin saukar gaggawa bayan ya nufi kasar Kazakhstan. Akwai mutum 29 da suka tsira.
Sanarwar da kamfanin ya fitar ta zo ne a daidai lokacin da wani fasinja da ya jikkata ya bayyana cewa sun ji wata ƙara ta fito daga waje a lokacin da suke tunkarara Grozny da ke kudancin Rasha.