Erdogan ya bayyana matukar sha'awar Turkiyya ga shirin janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Rasha a Karabakh, yana mai yaba wa kokarin Azarbaijan na sake ginawa da farfado da yankunan da aka kwato daga mamayar Armeniya.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya haɗu da takwaransa na Azerbaijan Ilham Aliyev domin tattaunawa a kan dangantakar ƙasashen, waɗanda suka haɗa da na yanki da na duniya, kamar yadda Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta sanar.

Erdogan da Aliyev sun gudanar da tattaunawa a Dandalin Shugaban Ƙasa da ke Ankara, inda suka tattauna kan abubuwa da dama waɗanda suka haɗa da "kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza, da sake gina wasu yankuna na Azerbaijan da aka 'yanta daga masu mamaya, da kuma ababe da dama waɗanda suka shafi yankin da duniya baki ɗaya,"

Erdogan ya bayyana matukar sha'awar Turkiyya ga shirin janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Rasha a Karabakh, yana mai yaba wa ƙoƙarin Azarbaijan na sake ginawa da farfaɗo da yankunan da aka ƙwato daga mamayar Armeniya.

Sanarwar ta kara da cewa, yayin da yake magana kan halin da Falasiɗnu ke ciki, Erdogan ya yi Allah-wadai da matakin da Isra'ila ta ɗauka, yana mai musu laƙabi da masu "ayyukan kisan kiyashi da ke barazana ga zaman lafiyar yanki da ma tsaron duniya."

"Erdogan ya sake nanata cewa mafita ta dindindin ta ta'allaƙa ne wajen kafa ƙasar Falasɗinu mai Gabashin Birnin Kudus a matsayin babban birninta, yana mai kira ga ƙasashen duniya da su matsa wa Isra'ila lamba ta dakatar da munanan manufofinta."

Erdogan ya kuma yaba wa matakin da Azarbaijan ta ɗauka na kafa ƙungiyar sada zumunta tsakanin 'yan majalisar dokoki da Jamhuriyar Cyprus ta Arewa ta Turkiyya (TRNC) a majalisar dokokinta. Ya bayyana cewa, "muhimmancin gayyatar shugaban TRNC Ersin Tatar zuwa taron ƙolin ƙungiyar ƙasashen Turkiyya da za a yi a Shusha, yana mai kallonsa a matsayin wani ci gaba ga al'amuran Cyprus," in ji sanarwar.

Bugu da kari, Erdogan ya nuna jin daɗinsa ga gayyatar Aliyev zuwa taron sauyin yanayi a kasar Azarbaijan, yana mai ba da cikakken goyon baya daga Turkiyya kan shirin. Ya bayyana muhimmancin abubuwan da suka shafi aikin tsaftace muhalli na Zero Waste Project, wanda Uwargidan Shugaban Ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ke jagoranta, wanda zai kasance wani bangare na taron.

TRT World