Aliyev ya bayyana dalilin da ya sa ya dauki matakai a yankin a lokacin da yake waya da Blinken. Hoto/Reuters

Azerbaijan ta tabbatar da cewa ta cimma yarjejeniya tsakaninta da ‘yan awaren Armenia domin kawo karshen ayyukan soji da take yi a Karabakh.

“Sakamakon rokon da wakilan mazauna Armenia da ke Karabakh suka yi, an cimma matsaya domin dakatar da matakan yaki da ta’addanci s ranar 20 ga watan Satumba da misalin 1:00 na rana,” in ji ma’aikatar tsaro a sanarwar da ta fitar.

Ofishin Shugaba Ilham Aliyev a wata sanarwa ta daban ta tabbatar da batun tattaunawa da ‘yan awaren kan sake hade Azerbaijan a ranar Alhamis a birnin Yevlakh.

An cimma matsaya bayan dakarun da ke wanzanar da zaman lafiya na Rasha da aka kai yankin sun shiga tsakani.

Ana ganin dakatar da ayyukan yaki da ta’addanci a matsayin wata hanya ta rage fargaba da kuma kawo zaman lafiya a Karabakh.

A karkashin wannan yarjejeniyar, za a raba duka kungiyoyi masu rike da makamai makamansu.

A wata tattaunawa ta talabijin, Firaiministan Armenia Nikol Pashinyan ya bayyana cewa “yana da muhimmanci” a tsagaita wuta da kuma fatan dakarun Rasha za su tabbata an aiwatar da yarjejeniyar.

Tun da farko dai Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev ya shaida wa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken cewa ba za su janye matakan da suka dauka na yaki da ta’addanci a Karabakh ba har sai idan dakarun Armenia sun ajiye makamansu.

Azerbaijan da Armenia wadanda a baya ke karkashin kungiyar Soviet na ta rikici da juna tun daga 1991 a lokacin da sojojin Armenia suka mamaye Karabakh, wanda yanki ne da duniya ta amince a matsayin daya daga cikin yankunan Azerbaijan.

Azerbaijan ta karbi akasarin yankin a lokacin yakin 2020 wanda ya kawo karshe bayan Rasha ta jagoranci wata yarjejeniyar zaman lafiya da kuma bude kofa domin dawo da abubuwa daidai.

AA