Duka bangarorin biyu sun amince su ci gaba da musanyar yawu./ Hoto: Reuters Archive

Ma’aikatar harkokin waje ta China ta ce, Amurka da China sun gudanar da tattaunawa ta ‘gaskiya da gaskiya’ a birnin Beijing, game da inganta alaka da kuma warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu.

Ita ma ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta ce, taron wani bangare ne na yunkurin da ake yi don cigaba da wanzar da hanyoyin hulda da gini kan tagomashin da aka samu a tattaunawar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

“Bangarorin biyu sun gudanar da tattaunawa ta gaskiya da gaskiya, kuma mai tattare da alfanu, domin habaka kokarin inganta dangantaka tsakanin China da Amurka,” a cewar ma’aikatar harkokin wajen China ranar Talata.

Mataimakin Sakataren Harkokin Waje na Amurka, mai lura da Asiya da yankin Pacific, Daniel Kritenbrink ya ziyarci Beijing wannan makon, a wata ziyarar China da ba a saba gani daga babban jami’in diflomasiyyan Amurka ba.

Amurka na neman rage takun-saka tsakanin kasashen biyu masu karfi a duniya.

Amurka ta bayyana tattaunawar ta Kritenbrink tare da mataimakin ministan harkokin waje na China, Ma Zhaoxu da kuma jami’in diflomasiyya Yang Tao, a matsayin “ta keke-da-keke kuma mai alfanu".

China ta ce bangarorin biyu sun tattauna kan “warware bambance-bambance bisa la’akari da matsayar da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu a taronsu na garin Bali, a watan Nuwamban bara".

Ma’aikatar harkokin wajen China ta kara da cewa, "Duka bangarorin sun amince su ci gaba da tattaunawa”.

'Batutuwa kamar na Taiwan'

Ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta ce, “bangarorin biyu sun yi musayar yawu game da alakarrsu, da batun mashigar ruwa, da hanyoyin tattaunawa, da wasu batutuwa,” wato yana nufin batun Mashigar Taiwan.

Ita ma China ta ce jami’an diflomasiyyarta sun “fayyace matsayar (China) game da manufofin kasa kamar na Taiwan", kasar da China ta ke ikirarin cewa yankinta ne, kuma ta sha alwashin karbe ta nan gaba, idan ta kama ta amfani da karfi.

Taron ya zo ne yayin da ake fuskantar takun saka tsakanin kasashen masu karfi game da Tekun Kudanci China Sea, gami da batun Taiwan da tarin wasu batutuwan takaddama.

Ranar Litinin, Amurka ta yi gargadin cewa abin da sojojin China suka yin a “nuna barazana” wanda ya kusa janyo yin karo tsakaninsu da rundunonin sojin Amurka a kan teku da sararin samaniya, zai iya haifar da asara rai ko dukiya a nan gaba.

A makon da ya gabata, gwamnatin Amurka ta ce Daraktan CIA, William Burns ya gudanar da wata ziyarar sirri zuwa China a watan Mayu, da nufin kyautata hanyoyin tattaunawa da gwamnatin China.

AFP