Lauyan da ke kare Omar da masu gabatar da kara sun amince da hukuncin daurin shekaru takwas a zaman da aka yi a ranar 19 ga watan Yuli  / Hoto: Reuters

An yanke wa mutumin da ya kai hari da gatari a wani masallaci a Toronto da ke Canada da nufin halaka mutane da dama hukuncin zaman kurkuku na shekaru takwas a ranar Talata.

Mutumin mai suna Mohammed Moiz Omar ya dauki maganin feshin kwari da gatari sannan ya kutsa kai cikin Masallacin Dar Al-Tawheed da ke Mississauga, inda masu ibada kusan 30 ke yin sallar asuba a ranar 19 ga Maris, 2022.

An dakatar da shi kafin ya kai ga aiwatar da mummunar aniyarsa ga jama'ar da ke sallah.

A cewar kotun, Omar "ya yi niyyar aikata laifi na halaka mutane da dama," kuma a fusace yake da tsananin kiyayya da niyyar cutar da Musulmai.

Ya yi imani cewa Musulunci "addini ne mai tsanantawa da tashin hankali."

A ranar 19 ga watan Yuli, Omar ya amsa laifuka guda uku: shirya amfani da wani abu mai cutarwa (gubar feshin kwari) a jiki da kai hari da makami da kuma barnata dukiyar mabiya addini.

Ya kuma amince cewa harin ya kunshi ayyukan ta'addanci. Yana da shekaru 24 a lokacin da ya shirya kai harin.

A yayin sauraron karar na ranar 19 ga watan Yuli, limamin masallacin, Ibrahim Hindy, ya ce harin na da muni sosai.

"Wannan ba mutumin da ke cikin mummunan yanayi ba ne ko kuma yake fama da wata lalura da ta shafi kwakwalwa," a cewar Hindy a yayin hirar da amfanin Watsa Labarai na Canada ya yi da shi.

"Wannan shi ne mutumin da ya tsara ainihin abin da yake son yi da kuma yadda yake son kashe Musulmai," in ji Hindy.

"Ina farin ciki kan yadda al’ummar cikin masallacin suka yi saurin dakatar da shi kafin ya kai ga cutar da wani."

Mutanen masallacin sun yi kokarin kai Omar kasa. Babu wanda ya ji wani mummunan rauni, ko da yake an kai wa mutum daya bugu a ciki, wasu da dama kuma sun sheki gubar feshin kwari da ya shigo da ita masallacin.

An kiyasta barnar da aka yi a masallacin kan dalar Canada 16,000 kwatankwacin dalar Amurka 12,140. Omar ya shaida wa ‘yan sanda cewa shi Musulmi ne amma a yanzu bai yarda da Allah ba.

Lauyan da ke kare Omar da masu gabatar da kara sun amince da hukuncin daurin shekaru takwas a zaman da aka yi a ranar 19 ga watan Yuli, kuma a ranar Talata alkali ya amince.

TRT Afrika