Donald Trump ya mulki Amurka a matsayin shugaban kasar na 45 tsakanin 2017 da 2021. Photo: AP 

An tuhumi tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan yunkurin soke sakamakon zaben shugaban kasar na shekarar 2020 bayan rikicin da magoya bayansa suka tayar a fadar gwamnatin Amurka.

Wannan dai na zama barazana mafi muni ta shari'a da tsohon shugaban ke fuskanta yayin da yake yakin neman sake komawa fadar White House.

Ana tuhumar Trump bisa aikata laifuka uku na hada baki da kuma kutse da ya yi cikin tuhume-tuhumen shafuka 45 da lauya na musamman Jack Smith ya gabatar wa wata kotu.

An zargi tsohon shugaban, wanda ke kan gaba a zaben fitar da gwani na jam’iyyar Republican na 2024, da hada baki don damfarar Amurka da hana gudanar da gudanar da harkokin gwamnati: taron hadin gwiwa na Majalisa da aka gudanar a ranar 6 ga watan Janairu, 2021 don tabbatar da nasarar zaben dan jam'iyyar Democrat Joe Biden a matsayin zababben shugaban kasar.

“Manufar wannan makarkashiya ita ce a soke sahihin zaben shugaban kasa na 2020 ta hanyar amfani da da’awar karya ta magudin zabe,” a cewar takardar karar da aka gabatar.

''Ci gaba da zama a kan karagar mulki''

Masu gabatar da kara daga bangaren gwamnatin tarayya sun ce Donald Trump ya ‘’kuduri aniyar ci gaba da zama a kan karagar mulki’’ cikin makircin da suka shafi "aikin gwamnatin Amurka, a tsarinta na tattarawa da kirgawa da kuma tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasa."

Rikicin da ya barke, ya haifar da tashin hankali a babbar birnin na Amurka a ranar 6 ga Janairun 2021, lokacin da masu zanga-zangar suka kutsa kai cikin ginin fadar gwamnatin kasar da karfi, suka kuma far wa jami'an 'yan sanda da ke wajen tare da tarwatsa taron kidayar kuri'un zabe.

A ranar Alhamis ne ake sa ran Trump zai gurfana a gaban mai shari’a Tanya Chutkan a Amurka.

TRT Afrika