Sojojin Isra'ila za su zauna a wurare biyar a Lebanon — Rundunar soji / Hoto: AA

Litinin, 17 ga Fabarairu, 2025

1438 GMT –– Rundunar sojan Isra’ila ta ce dakarunta za su ci gaba da kasancewa a “muhimman wurare” biyar a cikin Lebanon bayan ranar Talata, lokacin da wa’adin janye sojoji daga makwabciyarta ya ƙare, a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni da aka cim ma.

Matakin ya saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah. A karkashin yarjejeniyar, za a girke sojojin na Lebanon a kudancin kasar tare da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD yayin da sojojin Isra'ila suka janye na tsawon kwanaki 60 wanda daga baya aka tsawaita zuwa ranar 18 ga watan Fabrairu.

Kakakin rundunar sojin kasar Laftanar Kanar Nadav Shoshani ya shaida wa manema labarai cewa, bisa la’akari da halin da ake ciki a yanzu, za mu bar wasu kananan dakaru da aka girke na wucin gadi a wasu muhimman wurare guda biyar a kan iyakar kasar ta Lebanon domin mu ci gaba da kare mutanenmu da kuma tabbatar da cewa babu wata barazana nan take.

"Wannan wani mataki ne na wucin gadi har sai sojojin Lebanon sun sami cikakken aiwatar da fahimtar".

1205 GMT –– EU za ta gaya wa Isra'ila cewa dole mazauna Gaza su koma gida cikin mutunci

Kungiyar EU na shirin gaya wa Isra'ila a mako mai zuwa cewa Falasdinawa da aka kora daga gidajensu na Gaza ya kamata a tabbatar da dawowar su cikin mutunci kuma Turai za ta ba da gudunmawar sake gina yankin da ya ruguje, a cewar wata takarda da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.

Wani daftarin da ke bayyana matsayar kungiyar ta EU ya jaddada kudurin Turai na tabbatar da tsaron Isra'ila da kuma ra'ayinta na cewa "ya kamata mazauna Gaza da suka rasa matsugunansu su koma gidajensu cikin aminci da mutunci".

Kungiyar EU za ta ba da gudunmawa sosai ga kokarin hadin gwiwa na kasa da kasa don farfado da sake gina Gaza da wuri," in ji ta, tare da yin kira da a ba da cikakkiyar damar kai agajin jinƙai.

"Kungiyar EU ta yi matuƙar baƙin ciki game da adadin fararen hula da ba za a amince da su ba, musamman mata da yara, waɗanda suka rasa rayukansu, da kuma mummunan yanayin jinƙai, musamman sakamakon rashin isassun kayan agaji a Gaza, musamman a Arewa."

0604 GMT –– Majalisar tsaron Isra'ila na shirin tattaunawa kan zagaye na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Majalisar tsaron Isra'ila na shirin tattaunawa kan zagaye na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun amince da matsaya iri ɗaya da ke sukar Hamas da Iran.

Rubio ya je Isra'ila ne a matakin farko na ziyararsa a Gabas ta Tsakiya a matsayinsa na babban jami'in diflomasiyya na gwamnatin Shugaba Donald Trump, kuma zai tafi Saudiyya a ranar Litinin.

"Ba zai yiwu Hamas ta ci gaba da kasancewa fannin soji ko kuma dakarun gwamnati ba... dole a kawar da ita," in ji Rubio da yake magana a game da ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa wadda ta kwashe fiye da wata 15 tana gumurzu da Isra'ila a yankin Gaza kafin a amince da tsagaita wuta ranar 19 ga Janairu.

2257 GMT — Kashi 30 ne kacal na motocin kayan agaji ya isa Gaza a kwana biyu da suka wuce

Adadin manyan motocin da ke ɗauke da kayan agaji da suka shiga a kwanaki biyu da suka gabata bai wuce kashi 30 cikin ɗari ba, a cewar ofishin watsa labarai na Gaza, wanda ya ce hakan ya faru ne sakamakon katsalandan ɗin da dakarun Isra'ila suke yi a yunƙurin ganin an kai kayan agaji yankin.

Kawo yanzu manyan motocin kayan agaji guda 180 ne suka shiga Gaza, adadin da ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da motoci 600 da aka amince su shiga yankin a yarjejeniyar tsagaita wutar da aka ƙulla tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas, a cewar wata sanarwa da ofishin watsa labarai na Gaza ya fitar

Ƙarin labarai👇

2103 GMT — Rubio ya ce kasancewar ƙarin 'Isra'ilawa' a Gabas ta Tsakiya zai sa duniya ta ƙara 'zama lafiya'

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi iƙari ranar Lahadi cewa duniya za ta fi samun zaman lafiya idan aka samun ƙarin Isra'ilawa da ke zaune a yankin Gabas ta Tsakiya.

"Idan aka samu ƙarin Isra'ila a Gabas ta Tsakiya, duniya za ta fi zama lafiya da aminci," in ji Rubio a wani tarin manema labarai da ya gudanar da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Yammacin Birnin Ƙudus, a cewar wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Isra'ila ya fitar.

Kazalika ya jaddada aniyar mahukuntan Washington ta goyon bayan Isra'ila.

Falasɗinawa na zauna a ɓuraguzan gine-gine ko kuma kangwaye a birnin Khan Younis bayan Isra'ila ta rusa gidajensu/ Hoto: AA
TRT World