D Katse intanet da waya na nufin Falasɗinawan da ke zaune a Gaza da na sauran ƙasashe ba za su iya samun labaran waɗanda aka kashe da waɗanda ke raye ba. Hoto: AA

A ranar 14 ga watan Oktoba, mutum tara a cikin dangina suka mutu sakamakon wani harin sama da Isra’ila ta kai gidan Baffana Azmi Aljamal, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsa da matarsa da ƴaƴansa uku da jikokinsa uku da kuma wata ƴar ɗau”wana.

Yayana Abood ya samu isa gidan duk da ɗumbin matsalolin da ya fuskanta.

Ya shaida min cewa ya janye gawar Aljamal daga ƙarƙashin ɓaraguzai, “har a lokacin yana numfashi, yana da rai.”

Daga nan ne Abood ya sanar da mummunan labarin ga sauran danginmu ta hanyar aika mana saƙon kar-ta-kwana da na Whatsapp da kuma kiran iyayena ta waya.

Daga nan kuma zuwa ranar 27 ga watan Oktoba sai aka rasa ƴar damar da ake da ita ma ta sanarwa duniya halin da ake ciki na kisan Falasɗinawa a Gaza, bayan da aka yanke hanyoyin sadarwa na waya da intanet baki ɗaya a yankin wanda aka yi wa ƙawanya.

An toshe hanyoyin sadarwa da intanet da katse wutar lantarki da hana shigar da fetur ne bayan da Ministan Tsaro na Isra’ila Yoav Galant ya ba da umarni a farkon hare-haren da aka kai Gaza, inda har ya kira Falasɗinawa da cewa “dabbobi ne a fatar mutane” waɗanda ya kamata a hana su duk wani jin dadin rayuwa.

An mayar da irin waɗannan kalamai da ke da alaƙa da kisan ƙare dangi ba komai ba ne saboda yadda Ƙasashen Yamma suka ƙi yin tir da Isra’ila a kan cin zarafin Falasɗinawa da take yi, lamarin da a ƙarshe ya ba su damar kai harin bam kan asibitoci da sansanonin ƴan gudun hijira.

Karin killacewa

Katse intanet da waya na nufin Falasɗinawan da ke zaune a Gaza da na sauran ƙasashe ba za su iya samun labaran waɗanda aka kashe da waɗanda ke raye ba.

Yana nufin sanya Falasɗinawa a cikin wani irin baƙin rami. Duk wani bidiyo ko hoto da aka samu ya fito daga Gaza a cikin kwana biyar din da suka wuce yana nuna tasirin katse musu abubuwan more rayuwa da suke ciki.

Falasɗinawa na ɗaukar mutanensu da suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a kan amalanken jaki saboda ba za su iya samun motocin asibiti ko neman taimakon tawagogin agaji ba.

Ma’aikatan lafiya a Gaza suna bin duk wani waje da suka ji ihun mutane ne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da hare-haren suka rusa suna zaƙulo su.

Falasɗinawa da dama sun mutu saboda motocin asibiti ba sa zuwa daukar su a kan lokaci. Ƴan agaji kan garzaya ne a kan kekuna zuwa wajen tawagogin agaji suna gaya musu inda aka kai hari.

Saƙon Isra’ila a kan wannan rufewa ruf da ta yi wa Gaza a bayyane yake – yana nuna cewa Falasɗinawa ba su da ƴancin kai labarin ƴan uwansu da ke cikin yanayi ga ma’aikatan lafiya don ba su agaji ko kuma su gaya wa ƴan uwa da abokan arziki da ke wasu wuraren a fadin duniya labarin mutuwar don su yi alhini.

A ɗaya hannun kuwa, Falasɗinawa suna sake jin cewa mayan ƙasashen duniya masu yawan ikirarin kare hakkin ɗan’adam a yanzu sun gaza kare nasu hakkokin da ake takewa, inda suka zuba ido suna kallon wannan abin tsoro a wayoyinsu da talabijin ɗinsu.

Wani yaƙi na hulɗa da jama’a

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 8,796, tun bayan hare-haren ba-zata da Hamas ta kai a kan sansanonin sojin Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Aƙalla mutum 2,030 daga cikinsu har yanzu suna ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, ciki har da yara 900.

Daga cikin Falasɗinawa 8,796 da aka kashe tsakanin 7 ga watan Oktoba zuwa Nuwamba, mafi yawansu yara ne da mata, inda aka kashe yara fiye da 3,648 a Gaza.

A yayin da Isra’ila ke kallon yadda ake samun ƙaruwar goyon bayan Falasɗinawa a duniya, inda aka yi zanga-zangar yin tir da hare-harenta a Gaza, a manyan birane kamar London da Kuala Lumpur da Jakarta da Istanbul da Amman da Alkahira da New York da Chicago da Rome da sauran su, har yanzu da yawan Isra’ilawa na yarda da farfagandar ƙasarsu – cewa ko da kuwa za a kashe dubban Falasɗinawa fararen hula to ba komai ba ne in dai Isra’ila za ta samu tsaro.

A halin da ake ciki na yadda ake samun sauyi a irin kallon da duniya ke yi wa Isra’ila, inda mutane da dama ke ƙin yarda da farfagandarsu ta “kare-kai”, sai gwamnatin Isra’ilan ta katse sadarwa a Falasɗinu don ɓoye kisan kiyashin da take yi, da kare sojojinta daga caccaka, da samun ɗaurin gindin kafafen watsa labaran Amurka da Turai da kuma fitattun mutane, don janye hankalin duniya daga girman laifin da take aikatawa da kuma ɓoye halin da Falasɗinu ke ciki.

Amma ita gaskiya a ko yaushe ba ta ɓuya. Isra’ila ba za ta iya ɓoye girman laifukan da ta aikata a Gaza ba.

Falasɗinawa na ƙirga duk wata rai da suka rasa a mako huɗun da suka wuce, ba sa mantawa da lissafin duk wanda ya mutu a kisan kiyashin Isra’ila, daga na iyalan Alghoul da wani harin sama ya kashe musu mutum 80 a sansanin ƴan gudun hijira a Al Shati, da har yanzu ba a ciro kusan rabinsu daga ƙarƙashin ɓaraguzai ba, zuwa na Iyalan Aqel a sansanin ƴan gudun hijira na Jabaliya da su ma aka kashe mutum 85 a irin wannan harin, Falasɗinawa ba sa mantawa da kowanne.

Tasirin rufewa ruf

An shafe unguwar Tal Al-Hawa tas ta koma kufai, inda a nan ne Asibitin Al Quds yake, tare da kashe Falasɗinawa da dama. Asibitoci sun yi cikar kwari sannan aikin ya yi wa ma’aikatan yawa.

A ƙasa likitoci suke yi wa marasa lafiya tiyata sannan babu allurar saka mutane bacci idan za a yi musu tiyata.

A taƙaice dai Isra’ila ba ta son duniya ta ga wannan muguntar a zahiri saboda Tel Aviv da manyan ƙawayenta na Yammacin Duniya, ba za su iya ba da wata hujja ga mutanensu ta kisan da ake yi wa Falasdinawa a Gaza ba.

Me Isra’ila za ta yi? Kawai sai dai ta yi duk yadda za ta yi don rufe gaskiyar kisan Falasɗinawa da kuma aike wa al’ummar Gaza saƙon cewa za ta haɗa da yi musu kisan mummuƙe ba tare da an sani ba.

Isra’ila tana wasa da dokokin ƙasa da ƙasa, waɗanda Ƙasashen Yamma suke amfani da su kawai a lokacin da suke son kare muradunsu. A sakamakon hakan, Isra’ila gaba-gaɗi take kai hare-haren bam a kan inda duk take so.

Isra’ila tana kai hare-hare kan kasuwanni da rukunan shaguna da makarantu da ɗakunan karatu da masallatai da coci-coci da tituna da gidaje da filaye da asibitoci da sansanonin ƴan gudun hijira da ma duk wani waje da ya raya mata.

Su kuwa Falasɗinawa, abin ya zame musu tamkar cin karo da wani ƙaton dodo ne, illahirin birnin ya zame musu masifa. Sannan dakarun Isra’ila da ƙawayensu ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen sanyawa a ga farinta duk da tarin muguntarta.

Yousef M. Al JamalYousef M. Aljamal wani manazarci ne a Cibiyar Ilimin Ganas ta Tsakiya kuma ya fassara llittattafai da dama. Tare da shi aka wallafa littafin ‘A Shared Struggle: Stories of Palestinian and Irish Hunger Strikers’ na An Fhuiseog a watan Yulin 2021.

Togaciya: Ra’ayin marubucin ba dole ba ne ya yi daidai da ra’ayoyi da ka’idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT World