Tsakanin kudin China na yuan da dalar Amurka / Hoto: Reuters

Daga JONATHAN FENTON-HARVEY

Shiga tsakanin da China ta yi dangane da rashin jituwar kasashen Saudiyya da Iran a watan Maris, wani yunkuri ne na sulhunta bangarori biyu a siyasar duniya.

Bayan wannan nasarar a siyasance – ta samu damar karfafa tattalin arzikinta a duniya – China ta so ne ta dakile karfin da dalar Amurka ke da shi.

A baya kasashen Larabawa sun taba yunkurin fara amfani da wasu takardun kudi a tsakaninsu maimakon dala.

Lokacin shekarun karshe na mulkin marigayi Saddam Hussein, Iraki ta so ta fara sayar da manta da kudin yuro, Euro.

Hakazalika, Libiya ta so ta samar da wani kudi na bai-daya da zai samu kima daga zinare a shekarun 2000.

Sai dai babu wani babban yunkuri da ya yi nasarar dakile karfin dalar Amurka, matsin tattalin arzikin da duniya ta shiga a 2007-2008 ya sa an daina jin kiraye-kirayen rage amfani da dalar.

Sai dai ci gaban da China ta samu cikin hanzari ya sauya wannan. Mahukunta a China ba sa boye aniyarsu ta karya karfin dala, wanda zai sa a kara amfani da kudin China na yuan – ko kuma renminbi, kamar yadda wasu suke kiransa.

Yin hakan zai rage karfin tattalin arzikin Amurka – wanda da shi ne da kuma karfin soja da take da shi ya sa kasar take da karfin fada a ji a duniya.

China tana so ta daina amfani da dala ta fuskar tattalin arzikinta, saboda hakan zai rage barazana da Amurka take yi na sanya wa kasashe takunkumi karya tattalin arziki kamar wanda ta sa wa Rasha - wanda ya sa Rashar ta kara yawan kudin China da take ajiye da shi a ketare.

Saboda rasa karfin iko da Amurka take ci gaba da fuskantar a Gabas ta Tsakiya, hare-haren da Rasha take kai wa Ukraine suna ci gaba sauya siyasar yankin, saboda takunkuman da Amurka ta sanya wa Rasha ya sa kasashen yankin daukar bangare a rikicin.

Yakin Ukraine ya kara tuna wa kasashe cewa Amurka za ta iya kakaba musu takunkumi a kowane lokaci, sai wasu kasashe ciki har da wasu na yankin Gulf masu arzikin man fetur suka bijirawa Amurka kuma suka ci gaba da hulda da Rasha da kuma China.

Kuma saboda yadda China take da karfi ta fuskar kasuwanci, yakin ya kara wa China karfi ta fuskar tattakin arziki a yankin.

A karshe, karfin tattalin arziki daidai yake da karfi a siyance, karfin fada a ji da Amurka take da shi tun bayan karshen Yakin Cacar Baka ya samo asali ne daga yadda dalar Amurka ta kasance takardar kudin da kasashe suke ajiya da su a ketare.

Idan aka rage amfani da dala hakan yana nufin karfin fada a jin Amurka zai ragu.

Yiwuwar fara amfani da Yuan a Gabas ta Tsakiya

Wasu kasashe a yankin Gabas ta Tsakiya sun fara maraba da cinikayya da wasu takardun kudi bayan dalar Amurka – wannan ya samo asali ne saboda yadda China ta zama babbar mai harkokin huldar kasuwanci da kasashen yankin.

China ta zama babbar abokiyar kasuwanci a yankin Gabas ta Tsakiya – tana hulda da manyan kasashe kamar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Saudiyya da Iraki da kuma Iran.

Idan ka dauki UAE misali, wadda ta rage dogaro kan Amurka a shekarun 10 da suka wuce kuma ta mayar da kanta wata kasa da dole manyan kasashen duniya ta yi aiki da ita.

A watan Maris, kasar ta taimaka wajen kulla wata babbar yarjejeniyar iskar gas da kudin yuan tsakanin kamfanin kamfanin TotalEnergies da kamfanin mai na China.

Ba don Total kamfanin kasar Faransa ba ne, wato wata kasar Yamma, amma kuma saboda UAE ta shige gaba wajen bude sabon babin fara amfani da kudin yuan.

Wannan ya kawo sauyi sosai a yankin.

An ruwaito cewa Saudiyya ma tana magana da hukumomin China kan yiwuwar sayar mata da mai da kudin yuan bayan Shugaba Xi Jinping ya bukaci a yi hakan a watan Disambar 2022.

Amurka ce kasar da ta fi kowacce sayen man fetur din Saudiyya, yayin da ake daidaita dalar Amurka da farashin mai - wanda aka yi wa hakan lakabi da "petrodollar."

Wannan kansa ya bai wa Amurka karfin iko a Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC), hakan yana nufin hulda da Saudiyya yana da muhimmanci sosai ga manufofin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kai hatta bayan kudi, Saudiyya tana karbar kudin yuan yayin cinikayya – wanda kila take amfani da su wajen biyan kudaden kayan da ake shigo mata da su daga China, wannan kansa zai jawo raguwar karfin dalar Amurka.

Ko da yake kasashen yankin Gulf na cewa ba za su yi cinikayyar man fetur da dala ba, kuma suna maraba da hakan saboda kare darajar kudi da hakan ke samarwa.

Yayin da karfin tattalin arzikin China yake ci gaba da karuwa, rage hulda da Amurka da aka yi a yankin Gabas ta Tsakiya zai bude kofar fara amfani da yuan.

A watan Fabrairu, Iraki ta samar da shirinta na fara yin cinikayya da China da yuan, bayan kasar ta fuskanci karancin dalar Amurka a babban bankinta – wani abin ta da hankali ga kasar da ta dogara da arzikin man fetur.

China ta riga ta shiga gaban Amurka inda ta zuba jari sosai a fannin man fetur din kasar, wanda Amurka ta yi watsi da shi bayan karshen yaki.

Ba yuan kadai ba ne ya shiga kasuwancin yankin Gabas ta Tsakiya. A watan Janairu, Indiya da UAE tun tattauna yadda UAE za ta rika sayar wa Indiya kayayyakin da ba man fetur ba da kudin Indiya na Rupee (INR).

Kungiyar Kasashen yankin Gulf (GCC) ta bakın UAE su ne suke gaba-gaba wajen neman wannan sauyi don fadada tattalin arzikinsu.

Takunkumai da matsin lambar Amurka

Amfani da sabbin kudi abu ne da kasashen za su so, saboda yadda Amurka take amfani da dala wajen sanya wa kasashe matsin lambar siyasa, wanda manyan cibiyoyin kasuwancin duniya kamar Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya (IMF) - da wasu masu suka ke ganin su a wani bangare na manufofin kasashen wajen Amurka.

Takunkuman da aka sanya wa Rasha ya nuna cewa Amurka tana amfani da matsayin dala wajen tilastawa da hukunta kasashe.

Kamar Rasha, babban bankin Iran kansa ya shiga mawuyacin hali saboda takunkuman Amurka. Ya yi ma barazanar karya darajar kudin kasar don hakan zai taimaka masa wajen cinikayya tsakaninsa da kasashe, yayin da Amurkan take amfani da karfin dalar don bunkasa tattalin arzikinta.

Amfani da matsayin dala da Amurka take yi wajen karfin fada a ji ya yiwu ne lokacin da kasashe ba su da wani zabi.

Yanzu kasashen da Amurka take matsa musu ta fuskar matsin lambar kasuwanci suna da zabi.

Bayan kwashe shekaru na takunkuman Amurka, Babban Bankin Iran ya bayyana kudin yuan a matsayin daya daga cikin manyan kudaden kasuwanci.

Iran tana sayar wa China mai ta karbi yuan, kuma saboda matsin lambar kasashen, Iran tana shirin daina amfani da dala da yuro gaba daya, kuma ta rika amfani da yuan duk san da za ta yi cinikayya da China idan hakan zai yiwu.

Wasu kasashen yankin su ma sun nuna sha'awarsu ta rage wa Amurka karfin fada a ji ta fuskantar kasuwanci, inda wasu suke gani a matsayin katsalandan saboda agajin da suke bayarwa mai cike da siyasa.

A Tunusiya, wata kungiya mai goyon bayan gwamnati ta ce kasar na fatan shiga jerin kasashen Aljeriya da Masar da Saudiyya a jerin da aka yi wa lakabi da BRICS (Brazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu) wato kasashen da tattalin arzikinsu ke habbaka cikin sauri.

Yayin da babu tabbas ko za a amince da wannan bukata, masu adawa da kasashen yammacin duniya da hukumar IMF a Tunusiya sun ce sun fi so kasarsu ta karkata wajen hulda da China da wasu kasashe da tattalin arzikinsu ke bunkasa saboda ba za su rika tsoma baki a harkokin cikin gidansu ba.

Wasu masana suna ganin an kafa BRICS ne da niyyar zuwa gaba ta rage karfin fada a jin Amurka da kuma yadda kasashe za su rage amfani da dala. Kuma akwai yiwuwar wadannan muradai ne kasashen za su so su cimma.

A ranar 13 ga Afrilu, sabon Shugaban Brazil Lula da Silva ya yi kira ga kasashen da ke cikin BRICS su fito da wata sabuwar takardar kudi wadda za ta zama kishiyar dalar Amurka.

Ya ce "kowane dare ina tambayar kaina kan mene ne abin da ya sa duka kasashe za su rika cinikayya da dala" nan take wakilan China da Brazil suka fara tafi.

Ko da yake a yanzu za a iya cewa magana ce ta fatar baki, amma kuma wannan burin da suke da shi zai kara karfafa wa kasashe yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka gwiwa na yiwuwar su yi kasuwanci da takardar kudi daban idan suka shiga BRICS.

Kalubalantar dala

Duk da wadannan kalubalen da dala ke fuskanta, har yanzu tana da karfi sosai.

Yawancin cinikayyar kasuwanci da bashin kasa da kasa da wasu na'uka na kasuwanci ana yin su ne da dala.

Daga shekarar 2021 zuwa baya, kusan kashi 60 cikin 100 kudaden ajiyar kasashe a ketare suna ajiye ne a dala. Kuma cinikayyar man fetur a duniya - ana yin kaso 80 cikin 100 ne da dala.

China za ta fuskanci babban kalubale Idan za ta maye gurbin amfani da dala da yuan a duniya da kuma yankin Gabas ta Tsakiya.

Dole sai ta gamsar da manyan bankunan kasashe kan su ajiye kwatankwacin biliyan 700 na yuan kafin ya iya zama kudin da ake ajiya da shi a ketare, kamar yadda dala ta samu wannan matsayi.

Ko da yake yuan ba ya cikin jerin kudaden da darajarsu ba ta karye da sauri ba, hakan yana nufin dala ta fi shi tabbas ta fuskar daraja.

China tana bukatar gyara manufofin kudinta da kuma gamsar da manyan bankunan kasashe cewa yuan yana da matsayi daya da dala dangane da tabbacin darajarsa kuma daga nan ta mayar da kudin wanda za a iya cinikayya da shi a duniya.

Ko da yake ana alakanta kudin kasar da ta fi karfi a duniya da iko da asusun ajiyar ketare na duniya.

Kudaden Portugal daga kuma sai Spain sun taba zama su ne suka yawa a asusun, hakazalika kudaden Netherlands da Faransa a karni na 17 da na 18.

Birtaniya ta taba mayar da fan shi ne kudin da aka fi ajiya da shi a asusun ketare a karni na 19 da farkon karni 20 wadanda ake amfani da a kasashen da ke karkashin ikonta, kafin Amurka ta karbe kambun na zama kasa mafi karfi a duniya.

Zancen gaskiya komai zai iya faruwa zuwa gaba kuma abubuwa za su iya sauyawa. Ko da yake, a yanzu, kasashe da dama suna da damar amfani da kudin kasashen daban-daban kamar yuan da kuma dala.

China ta hango wata dama ce yayin karfin fada a jin Amurka yake raguwa kuma wannan na faruwa ne saboda yadda tattalin arziki China ya habbaka a cikin fiye da shekaru 20 da suka wuce.

Masana da yawa sun yi hasashen tattalin arzikin China zai zarta na Amurka karfi nan da shekarar 2050.

Idan China ta zama kasar da ta fi karfin tattalin arziki a duniya hakan zai zama dalilan da za su sa a yi zancen wadda ya kamata ts yi iko da asusun ajiyan ketare na duniya.

Wani arashi kuma shi ne yadda hakan zai faru shekara daya bayan cikar jam'iyyar Kwaminisancin China ta cika shekara 100 da kafuwa wato a 2049, wanda Shugaba Xi Jinping ya bayyana a matsayin wani mataki da kasar za ta kai na karfin iko a duniya da kuma fada a ji.

A kula: Wannan ra'ayin marubucin ne kuma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT ba ne.

Jonathan Fenton-Harvey Jonathan Fenton-Harvey dan jarida ne kuma mai nazari, wanda ya mayar da hankali kan harkokin siyasa da manyan matsalolin da suka shafi al'umma a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. @jfentonharvey

TRT World