| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Ghana za ta fara aiwatar da shirin shiga ƙasar ba tare da biza ba ga dukkan 'yan Afirka
Shugaba Mahama ya bayyana manufar a lokacin ziyara ta farko ta Shugaban ƙasar Zimbabwea Shugaba Emmerson Mnangagwa ya kai Accra, in ji ministan harkokin wajen Ghana Sam Okudzeto Ablakwa.
Ghana za ta fara aiwatar da shirin shiga ƙasar ba tare da biza ba ga dukkan 'yan Afirka
Hukumomi sun ce an tsara shirin ne domin daidaita harkar shiga ƙasar da kuma tabbatar da kiyaye kan iyakokin ƙasar. / Others
2 awanni baya


Ghana ta zama ƙasa ta biyar a nahiyar Afirka da ta zaɓi bin tsari na shiga ƙasarta ba tare da buƙatar biza ba ga dukkan ‘yan ƙasashen Afirka, in ji wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen ƙasar.

Manufar, wadda Shugaba John Mahama ya bayyana, za ta fara aiki ne daga ranar 25 ga watan Mayu, wadda za ta zo daidai da bukukuwan ranar Afirka ta Duniya.

Shugaba Mahama ya bayyana manufar a lokacin ziyara ta farko ta Shugaban ƙasar Zimbabwea Shugaba Emmerson Mnangagwa ya kai Accra, in ji ministan harkokin wajen Ghana Sam Okudzeto Ablakwa.

Manufar ta ginu ne a kan wani shiri da aka yi a baya a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Nana Akufo-Addo, wanda ya yi shelar tafiye-tafiye ba tare da biza ba ga dukkan masu fasfo ɗin Afirka a jawabinsa na ƙarshe kan yanayin da ƙasar ke ciki a watan Janairun shekarar 2025.

Matakin, wanda aka sa ran cewa zai fara aiki a shekarar 2025, bai kankama ba kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa.

Da wannan matakin da aka ɗauka, Ghana ta bi sahun ƙasashen Afirka ‘yan kaɗan da suka haɗa da Benin da Gambia da Rwanda da kuma Seychelles waɗanda sun riga sun fara ba da damar shiga ƙasashen ga dukkan ‘yan Afirka ba tare da biza ba, lamarin da ya nuna gagarumar sauyi a tsarin tafiya da shige da ficen ƙasar Ghana.

Shirin na shiga ƙasa ba tare da biza ba, zai kasance wani ɓangare na garambawul da ake yi ga tsarin shige da ficen ƙasar Ghana, ciki har da gabatar da wata sabuwar kafa ta ba da biza ta intanet wadda ake tsammanin za a ƙaddamar da ita a cikin wata mai zuwa.

Hukumomi sun ce an tsara shirin ne domin daidaita harkar shiga ƙasar da kuma tabbatar da kiyaye kan iyakokin ƙasar.

Ablakwa ya ce manufar na da burin sake tabbatar da matsayin ƙasar na kasancewa cibiyar kishin ‘yan Afirka a ko ina, tare da buɗe hanyar samun ribar yawon buɗa ido da kuma cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka.

Ya ƙara da cewa tsarin na rashin buƙatar biza zai kasance wani ɓangare na ba da biza ta intanet da gwamnatin Mahama za ta ƙaddamar a wata mai zuwa.

Gwamnatin ƙasar Ghana tana kuma faɗaɗa damarmakin tafiye-tafiye ga ‘yan ƙasarta.

Ma’aikatar harkokin wajen ta ce ta ƙulla yarjejeniyoyin kawar da buƙatar biza 23 ga masu riƙe da fasfo ɗin Ghana tun shekarar da ta gabata.

Ana sa ran ƙaddamar da tsarin shiga ƙasar wa ‘yan Afirka ba tare da buƙatar biza ba zai taimaka wa ƙarin tafiye-tafiye a faɗin nahiyar, da yiwuwar tasiri kan harkar yawon buɗe ido da kasuwanci da ƙuma haɗin kan yankin.

Matakin ya yi daidai da ƙoƙarin da ake na nahiya na sauƙaƙa tafiye-tafiye a ƙarƙashin shirye-shirye irin su tsarin cinikayya ba tare da haraji ba tsakanin ƙasashen nahiyar Afirka (AfCFTA).