Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya sha alwashin gina matatar mai mai tace gangar ɗanyen mai 650,000 a ko wace rana a Gabashin Afirka irin wadda ya gina a Nijeriya muddin ya samu goyon bayan gwamnatocin yankin.
Dangote ya bayyana haka ne ranar Alhamis a taron zuba jari kan ababen more rayuwa na Afirka na shekarar 2026 ( Africa We Build Summit) da aka yi a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.
“Zan iya ɗaukar alƙawari ga shugabanni biyun da suka kasance a nan, idan suka goyi bayan matatar man, za mu gina irin wadda muke da ita a Nijeriya ,” in ji Dangote.
Hamshaƙin attajirin ya jaddada buƙatar “samar da cin gashin kai” ga ƙasashen Afirka a fannin makamashi.
Dangote ya ce an riga an fara aiki domin faɗaɗa ƙarfin matatar mansa ta Nijeriya domin ta iya tace gangar mai miliyan 1.4 a ko wace rana.

“Muna gina waccan (matatar Nijeriya) domin ƙara girmanta zuwa mai tace gangar ɗanyen mai miliyan 1.4 a ko wace rana kuma za ta kasance matatar mai mafi girma a duniya,” in ji shi.
Babban ɗankasuwar ya ce matatar da za ta kai kimanin kashi 10 na ƙarfin tace man Amurka za ta tallafa wa masana’antu na ƙere-ƙere.
Ranar Alhami, Shugaban Kenya William Ruto ya ce ƙasashen Gabashin Afirka suna tattaunawa kan shirin gina matatar mai ta haɗin gwiwa a tashar jirgin ruwa ta Tanga da ke Tanzania domin biyan buƙatar ƙasashen yankin.
Ruto, wanda ya halarci taron, ya ce matatar za ta tace mai daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da (DRC) da Kenya da Sudan ta Kudu da kuma Uganda.
“Za mu samu matata ta haɗin gwiwa a Tanga domin amfanar dukkanmu ta yadda wannan matatar za ta ɗauki dukkan mai daga DRC da Kenya da Sudan ta Kudu da kuma Uganda,” in ji shi.
Dangote ya kuma ce dole Afirka ta ba da fifiko ga ƙera abubuwa a cikin gida da kuma inganta masana’antu, yana mai gargaɗin cewa dogaro ga ababen da aka ƙera daga ƙetare na jefa tattalin arzikin ƙasashen nahiyar cikin barazanar rashin tabbas a samar da abubuwa da kuma na farashi.










