Wasu masu mamaya kusan 150 na Isra'ila sun kutsa cikin Masallacin Ƙudus a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye ranar Lahadi ƙarƙashin rakiya da kariyar 'yansanda mai yawa, kamar yadda rahotannin kafofin watsa labaran Falasɗinu suka ce.
Kamfanin dillancin labarai na hukuma, Wafa, ya rawaito, yana mai ambaton Gwamnatin Birnin Kudus, cewa sojojin mamaya sun shiga wurin da ake yawan rikici ta ƙofar Mughrabi, inda suka yi zagaye na tsokana a harabar wurin.
Shafin intanet na Al-Qastal, wanda ke mai da hankali kan al'amuran Birnin Ƙudus, ya ce masu mamaya sun aiwatar da ayyukan addinin Talmud yayin kutsen.
‘Yansandan Isra'ila sun sanya takunkumi kan shigar masu ibada na Falasɗinu a matsayin wani ɓangare na matakan da ake ɗauka don iyakance damar su ta zuwa masallacin.
Masallacin Ƙudus shi ne wurin ibada na uku mafi tsarki ga Musulmai a duniya. Yahudawa suna kiran wannan yanki da Temple Mount, suna ikirarin cewa shi ne wurin da haikalin Yahudawa guda biyu suka kasance a zamanin da.
Keta doka a masallacin
Tun daga 2003, 'yansandan Isra'ila sun ba da izinin masu mamaya su shiga masallacin kowace rana a lokuta biyu, lokacin sallar asuba da na magariba — ban da ranakun Jumma'a da Asabar.
Sashen Waqf na Musulunci a Birnin Ƙudus, wanda ke kula da masallacin, ya yi kira sau da yawa a dakatar da waɗannan kutse-kutsen, amma hukumomin Isra'ila ba su mayar da martani ba.
Tun bayan Itamar Ben-Gvir ya zama Ministan Tsaron Kasa na Isra'ila a ƙarshen 2022, an samu ƙaruwa a keta hakkoki a masallacin.
Falasɗinuawa na cewa Isra'ila na ƙara ƙoƙarin Yahudantar da Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye, ciki har da Masallacin Ƙudus, da kuma goge asalinsa na Larabawa da Musulunci.
Falasɗinuawa na ɗaukar Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye a matsayin babban birnin ƙasarsu ta gaba, bisa ga kudurorin ƙasa da ƙasa waɗanda ba sa gane mamayar Isra'ila ta birnin a 1967 ko haɗewar da ta yi a 1980.










