Pakistan ta ƙarfafa ƙoƙarin diflomasiyya don ƙulla yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran, inda Shugaban Rundunar Soja ƙasar, Asim Munir ya yi tattaunawa a matakin ƙoli a Tehran a wani ɓangare na sabon yunƙurin farfaɗo da tattaunawar ta kakare.
Munir ya gana da shugaban majalisar, Iran Mohammad Bagher Ghalibaf, wanda ake ganin shi ne babban mai sasantawa na Tehran, ‘yan kwanaki bayan da ya karɓi jakadun Iran da na Amurka a Islamabad.
Zagayen farko na tattaunawar ya ƙare ba tare da cim ma yarjejeniya ba, amma ɓangarorin biyu sun nuna shirin ci gaba da tattaunawar.
Jami’an Pakistan sun ce wata tawagar ƙwararru daga Washington da Tehran suna ci gaba da musayar bayan-fage, inda ɓangarorin biyu ke nufin mayar da zagayen tattaunawar na gaba ya zama na “sanya hannu kan yarjejeniya”.
Ba a tabbatar da ranar ba, duk da cewa fadar White House ta nuna alamun Islamabad ne wajen da za a yi. Islamabad, wadda ta sasanta tsagaita wuta na makonni biyu a ranar 8 ga Afrilu, na ƙoƙarin gina “fahimta mafi girma” tsakanin ɓangarorin.
Yaƙin, wanda ya ɓarke bayan hare-haren Amurka da Isra’ila a ƙarshen Fabrairu, ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 3,300 a Iran, tare da tagayyara dubban mutane daga gidajensu.
Batun nukiliya ne jigon tattaunawar
A tsakiyar tattaunawar akwai shirin nukiliyar Iran, wanda shi ne babban cikas ga cim ma yarjejeniya mai ɗorewa.
Majiyoyi daga Pakistan sun ce Tehran ta amince a ƙa’idance wan wani shiri na sa-ido daga ɓangare na uku kan ayyukan nukiliyarta, wanda zai iya haɗa ƙasashe huɗu, tare da Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Duniya (IAEA).
Washington ba ta amsa a hukumance ba tukuna, amma tana ci gaba da buƙatar takunkumai masu tsanani da dogon lokaci, kan haɓaka uranium na Iran.
A cewar rahotanni, Amurka na neman a dakatar da haɓaka uranium har zuwa shekaru 20 a madadin sassauta takunkumi, yayin da ake cewa Iran na iya la’akari da ɗan gajeren lokacin dakatarwa.
Iran ta kuma nemi tabbacin cewa ba za a sake kai mata hari daga Amurka ko Isra’ila ba, a matsayin wani ɓangare na kowace yarjejeniya.
Shigo da Qatar
A halin da ake ciki, Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya gana da Amir na Qatar, Tamim bin Hamad Al Thani don samun goyon bayan yankin wajen rage tashin hankali.
Shugabannin biyu sun jaddada buƙatar daidaita kasuwannin makamashi da tabbatar da amincin jigilar kaya yayin rikicin.
Qatar, babbar mai fitar da iskar gas ta LNG, ta riga ta ji tasirin rikicin bayan da aka samu katsewar samarwa a baya, wadda ake dangantawa da hare-haren da Iran ta kai.
Yayinda aikin diflomasiyya ke ƙaruwa, ana ƙara sa ran cewa sabon zagayen tattaunawar Amurka da Iran zai iya gudana a cikin ‘yan kwanaki, abin da ke ɗaukaka kyakkyawan fata kan warware rikicin ta hanyar sulhu.





