| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
UEFA ta yi watsi da korafin Barcelona kan wasan da Atletico Madrid ta doke su
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA, ta yi martani kan ƙorafin da Barcelona ta yi kan hukucin alƙalin VAR bayan da aka taɓa ƙallo da hannu a wasan gasar Zakarun Turai da Atletico Madrid ta doke Barca.
UEFA ta yi watsi da korafin Barcelona kan wasan da Atletico Madrid ta doke su
Barcelona ta sha kokawa kan rashin adalcin alkalan wasa. / Reuters
14 Afrilu 2026

Hukumar UEFA ya yi fatali da ƙorafin da Barcelona ta shigar dangane da wani hukuncin alƙalin wasa da ya haifar da cecekuce, yayin wasan kwatafainal na gasar Zakarun Turai zagaye na farko.

Atletico Madrid ta doke Barcelona, amma sai Barca ta nemi a gudanar da bincike kan ƙwallon da ɗanwasan Atletico, Marc Pubill ya ɗauka da hannu a cikin da’irar 18 bayan da golansa ya bugo masa.

Sai dai duk da taɓa ƙwallon da hannu, alƙalin wasa, Istvan Kovacs bai hukunta shi ba, balle ya bai wa Barca bugun ɗurme. Sannan alƙalin bidiyon VAR, Christian Dingert, shi ma bai zaɓi ya duba lamarin ba.

Barcelona ta koka kan cewa, kasancewar da ma Pubill yana da yalon kati a kansa, rashin duba lamarin da alƙalin VAR bai yi ba, abu ne da ya saɓa wa dokokin ƙwallo, kuma ya yi tasiri matuƙa kan ƙarshen wasan.

UEFA ba ta ɓata lokaci ba wajen yanke hukuncin cewa kukan da Barca ta yi. Kwamitin Ɗa’a da Ladabtarwa ya duba bahasin da aka gabatar, kuma ya yanke cewa babu tushen ci gaba da sauraron ƙorafin.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, hukumar ta ce: "Bayan wasan kwatafainal na Zakarun Turai UEFA zagayen farko tsakanin Barcelona da Atlético, Barcelona ta shigar da koke dangane da hukuncin alƙali. Kwamitin UEFA na Ɗa’a da Ladabtarwa ya yanke cewa koken ba abin karɓa ba ne."

A yanzu dai Barcelona za ta mayar da hankali kan dabarun rama ƙwallaye biyun da Atletico ta zura mata a zagayen farko, inda za su kara a zagaye na biyu a gidan Atletico yau Talata, don neman gurbi a wasan semifainal na gasar ta Zakarun Turai.