Ƙasar Scotland ta buga takardun kuɗi don murnar ƙwallon da Scott McTominay ya ci da watsewa, wadda ta kai su ga nasarar zuwa gasar Kofin Duniya ta bana.
Babban Bankin Scotland ya gabatar da taƙaitattun adadin takardun kuɗin na fam £20, waɗanda ke ɗauke da hoton da aka zayyana daga hoton ɗanwasan kasar, McTominay.
Shugaban hukumar gudanarwa ta bankin, Emma Noble ta faɗi haka, tana jaddada muhimmancin wannan nasara ga ƙasar ta Scotland.
Rabon da Scotland ta buga gasar Kofin Duniya tun shekarar 1998. A yanzu za ta kara da ƙasashen Haiti, Morocco, da Brazil, a Guruf C.
McTominay ya ci ƙwallo ne da watsewa ta baya, inda ya bai wa ƙasarsa nasara kan Denmark, kuma suka samu cancantar zuwa gasar FIFA 2026 da za a yi a Amurka, Canada, da Mexico.
Ɗan shekaru 29, Scott McTominay yana buga wa Napoli ta Italiya, kuma a baya ya buga Manchester United wasa.
Sai dai takardun kuɗin guda 100 kawai aka buga, inda 50 cikin adadin za a ba da su ta hanyar masu yin gwanjo ga masu son tara fitattun abubuwa, da kuma ta ‘yar-tinke a biranen Glasgow da Edinburgh.
Daga cikin kuɗaɗen da za a tara, za a ba da tallafi ga ƙungiyar Crisis Scotland, mai taimakon marasa galihun da ba su da matsuguni.












