Afirka ta Kudu tana da mafi kyawun jami'o'i a Afirka. Kamar yadda sabon kimanta matsayin Jami'o'in QS na Duniya, wanda ke nuna cewa ƙasar tana da jami'o'i takwas daga cikin manya 10 a nahiyar.
Za mu gaya muku sharuɗɗan da aka yi amfani da su wajen auna mtsayin jami’o’in. Amma da farko, bari mu duba manyan jami'o'in da ke kan gaba.
Auna matsayi na QS na 2027, wanda aka fitar a farkon watan Yunin 2026, ya nuna cewa Jami'ar Cape Town ce babbar jami'a a Afirka. Tana matsayi na 184 a duniya.
Kodayake tana riƙe da babban matsayinta a Afirka, ta sakko daga matsayinta na 150 a baya a duniya.
An kafa Jami'ar Cape Town a 1829 a matsayin Kwalejin Afirka ta Kudu, daga baya ta zama jami'a mafi tsufa a Afirka a 1918. An san ta da binciken likitanci da fafutukar yaƙi da wariyar launin fata, jami'ar yanzu tana cakuɗa tarihi da tasirin duniya waje guda.
A cikin jerin matsayi a Afirka, Jami'ar Johannesburg, Jami'ar Stellenbosch, Jami'ar Witwatersrand da Jami'ar Pretoria suna biye da ita bi da bi.
Jami'ar Amurka da ke Alkahira, Masar ce ta shida, inda Jami'ar Ain Shams, wacce ita ma take a Masar, take a matsayi na bakwai.
Jami'o'i uku da suka shiga 10 da ke sawun gaba suma suna Afirka ta Kudu. Su ne Jami'ar KwaZulu-Natal a matsayi na takwas, Jami'ar Rhodes a matsayi na tara, yayin da Jami'ar Afirka ta Kudu, UNISA, ke matsayi na goma.
Ka’idojin auna matsayin jam’o’in
Shin kuna mamakin me ya janyo haka?
To, binciken duniya yana amfani da "mahanga" guda biyar masu auna abubuwa daban-daban.
Bincike da Gano sabbin abubuwa ne babban abin da ke haifar da kashi 50% na maki. Wannan ya haɗa da suna a fannin ilimi da ambaton aiki, auna sakamakon bincike da tasirinsa.
Samun damar aiki da sakamako suna ba da kashi 20% na maki, gami da suna ga ma'aikata da nasarar tsofaffin ɗalibai da tasirinsu.
Wani abu kuma shi ne Kwarewar Koyo, wanda ya kai kashi 10%. Wannan ya haɗa da tallafin koyarwa.
Abu na huɗu shi ne Motsa Duniya, wanda ke ɗauke da kashi 15% na maki. Wannan ya haɗa da hanyoyin sadarwa na bincike na ƙasa da ƙasa bisa ga marubutan haɗin gwiwa tsakanin iyakoki, da kuma yawan ɗalibai na ƙasashen duniya.
Dorewa shi ne abu na biyar. Yana samar da kashi 5% na mahangar. Wannan ya mayar da hankali kan al'amuran muhalli, zamantakewa da shugabanci, shirye-shiryen harabar jami'a da bincike don Manufofin Ci Gaba Mai Dorewa na Majalisar Dinkin Duniya.
Baya ga manyan jami'o'i goma, jami'o'in Yammacin Afirka su ma suna ci gaba. Jami'ar Ibadan ta Najeriya da Jami'ar Lagos duk suna cikin matakin duniya na 1001-1200. Su ne mafi kyau a yankin kudu da hamadar Sahara baya ga Afirka ta Kudu.
A cewar binciken, Cibiyar Fasaha ta Massachusetts ita ce ta fi kowacce a duniya.











