Jam'iyyar da ke mulki a Kamaru ta kira wani taron manyan shugabanninta a ranar Laraba yayin da tambayoyi suka taso game da rashin ganin Shugaba Paul Biya, mai shekaru 93, wanda ya shafe kwanaki 45 a ƙasar waje.
Biya ya bar Kamaru a ranar 7 ga watan Yuni a tafiyar da ma'aikatan fadar gwamnatinsa suka bayyana a matsayin "hutu na wani ɗan lokaci a Turai" kuma tun daga lokacin bai dawo ba. Kuma gwamnati ba ta yi wani karin bayani ba game da lokacin da zai dawo ba.
Babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Democratic Movement ta Kamaru (CPDM) Jean Nkuete, wanda ya kira taron, bai bayyana makasuɗin taron ba, sai dai a wata sanarwa da aka fitar ya bayyana cewa za a yi wani "muhimmin zama na aiki."
Babu wata alama nan take da ke nuna cewa taron yana da alaƙa da rashin ganin Biya a bainar jama'a.
Tafiyar Shugaba Biya zuwa ƙasar waje ta yanzu ita ce mafi tsawo da ya taba yi, bayan irinta da ya yi a shekarar 2024, sannan gwamnati ta haramta tattaunawa kan rashin lafiyar Biya.
Sabon mukami na mataimakin shugaban ƙasa
Wannan bai hana wasu 'yan adawa yin tsokaci game da rashin ganin Biya ba.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar 18 ga Yuli, jam'iyyar adawa ta Kamaru, wato Jam'iyyar Democratic Union, ta yi kira ga jami'an gwamnati da su fito su "ba wa ƙasar cikakkun bayanai game da halin da ake ciki."
Sai dai mai magana da yawun gwamnati bai yi tsokaci kan wannan kira ba.
Kazalika gwamnati ta yi watsi da rahotannin da ke cewa Biya yana karɓar magani kuma ta ce zai iya tafiyar da harkokin ƙasar yadda ya kamata daga ƙetare.
A watan Afrilu ne 'yan majalisar dokokin ƙasar suka amince da buƙatar sake mayar da muƙamin mataimakin shugaban ƙasa, wanda shi zai zama na farko a jerin waɗanda za su gaji Biya, sai dai babu wanda ya samu muƙamin.
Haka kuma Biya bai naɗa sabuwar majalisar gwamnatinsa ba duk da cewa ya sake lashe zaɓen shugabancin kasar a watan Oktoban da ya wuce.
















