An tsammanin darajar kuɗin Ghana za ta faɗi a kan darajar kuɗin dala a cikin mako mai zuwa, zuwa ranar Alhamis, yayin da ake tsammanin na Uganda ya ƙarfafa kuma na ƙasashen Zambia da Nijeriya da Kenya za su sauya ɗan kaɗan ne, in ji ‘yancanji.
Ghana
Darajar kuɗin cedi ta Ghana za ta iya faɗuwa yayin da buƙatar kuɗaɗen ƙetare na kamfanoni ya ke ci gaba da wuce samuwar kuɗin.
Alƙaluma daga LSEG sun nuna cewa ana sayar da dala ɗaya kan cedi 11.00, idan aka kwatanta da 10.90 da aka sayi ko wace dala a makon da ya gabata.
"Kuɗin cedi ya shiga sabon matsi da ƙaruwar buƙatar dala daga kamfanoni na cikin gida da na ƙetare," in ji Ronald Mensah, wani ɗan canji a bankin Stanbic Bank na Ghana.
"Muna tsammanin dala za ta ci gaba da yin ƙaranci, inda kasuwar sayar da kuɗaɗen ƙetare (ta babban bankin ƙasar) ta kasance inda aka fi samun kuɗin," in ji shi.
Wani ɗan canjin kuma ya ce sakamakon cinikin kuɗaɗen ƙetare na babban bankin ƙasar, inda aka nemi siyan dala miliyan $399 maimakon dala miliyan $125 da aka gabatar, ya nuna ƙarin buƙatar dala.
Uganda
Ana ganin kuɗin Shilling na Uganda zai tsaya yadda yake idan aka kwatanta da dala, sakamakon yadda kuɗaɗen ƙetare za su shigo a ƙarshen wata daga ƙungiyoyin agaji da masu fitar da kayayyaki.
Bankuna sun bayyana cewa an sayar da dala ɗaya kan kuɗi 3,715/3,725 , idan aka kwatanta da yadda take a makon da ya gabata kan shilling 3,705/3,715.
Zambia
Kuɗin Kwacha na Zambia ma ana ganin zai tsaya yadda yake, bisa taimakon farashi mai ƙarfi na jan ƙarfe.
Kuɗin bai wani sauyawa ba sakamakon zaɓukan ƙasar na makon da ya gabata, inda Shugaba Hakainde Hichilema ya samu wa’adi na biyu duk da cewa jagoran ‘yanadawa ya ce zai ƙalubalanci sakamakon zaɓen.
A ranar Alhamis, bankunan ƙasar sun bayyana kwacha 18.99 a matsayin farashin dala ɗaya daga kwacha 18.98 da ya kasance a ranar Laraba da ta gabata, rana ɗaya kafin zaɓen.
Nijeriya
Kuɗin naira na Nijeriya shi ma zai iya kasancewa yadda yake ba tare da sauyi ba, sakamakon kuɗaɗen da ke shigowa na masu zuba jari daga ƙetare.
An sayar da dalar Amurka kan naira 1,345 a kasuwar musayar kuɗaɗe ta gwamnati ranar Alhamis, idan aka kwatanta da naira 1,358 a makon da ya gabata.
Ana sayar da dala a kasuwar bayan fage ne kan naira 1,410.
"Ina tsammanin matakin (sauyin) kudin zai kasance tsakanin naira 1,348 zuwa naira 1,360 a makongobe," in ji wani ɗancanji. "An sami shigar kuɗaɗen ƙetare da kyau zuwa cikin kasuwar."
Kenya
An tsammanin kuɗin shilling na Kenya zai ci gaba da kasancewa yadda yake tun da.
Bankuna a ƙasar sun ambato farashin dalar Amurka a kan shilling 129.30/50, wanda a ya ƙarƙare ranar Alhamis da ta gabata kan shilling 129.15/35.
















