Rundunar ’yansandan Jihar Katsina a Nijeriya ta tabbatar da mutuwar fitaccen malamin addinin Musulunci nan Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka, da abokinsa, Adamu Abubakar, bayan wasu ’yanbindiga sun kai musu hari a jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yansandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar a cikin daren Litinin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:30 na daren Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, a kofar gidan malamin da ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma.
Sanarwar ta ce wasu mutane biyu ɗauke da makamai, waɗanda ke kan babur ne suka buɗe musu wuta, inda suka ji wa malamin da abokinsa raunuka masu tsanani.
Bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’in ’yansanda mai kula da sashen Dutsin-Ma ya jagoranci tawagar jami’ai zuwa wurin, inda aka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti mafi kusa domin neman agajin gaggawa, kamar yadda sanarwar ta fada.
Sai dai yayin da likita ya duba su ya tabbatar da rasuwarsu, in ji kakakin rundunar ʼyansandan ta Katsina.
Kwamishinan ’yansandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an rundunonin musamman da na gudanar da ayyuka zuwa yankin domin taimaka wa bincike da kamo waɗanda ake zargi da kisan, a cewar kakakin ʼyansandan na Jihar Katsina.
Rundunar ta ce tuni aka fara bincike, yayin da ake ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda ake zargin, waɗanda suka tsere bayan aikata laifin.
Kwamishinan ’yan sandan ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, abokansu da mabiyansu, da kuma al’ummar ƙaramar hukumar Dutsin-Ma bisa wannan babban rashi.
Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da an kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar za ta sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da aka samu kan lamarin a nan gaba.
Sheikh Yahya Masussuka dai ya shahara da sukar wasu malaman Nijeriya da yake da sabanin fahimta da su, tare da kira da a bi Alkurʼani shi kadai, inda yake sukar wasu hadisai, wadanda a cewarsa bai kamata a danganta su ga Manzon Allah SAW ba.


















