| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Turkiyya na shirin zuba jarin dala biliyan 2 a sufurin sama da na sararin samaniya cikin shekaru uku
Tsarin kashe kuɗi na shekara uku na Ankara ya mayar da hankali ne kan kayayyakin sufurin sama da ayyuka na sararin samaniyan ƙasa da kuma kasuwantar da fasahar da aka samar daga cikin gida.
Turkiyya na shirin zuba jarin dala biliyan 2 a sufurin sama da na sararin samaniya cikin shekaru uku
Tauraron ɗanAdam na Turksat 6A shi ne tauraron ɗan Adam na sadarwa na farko da aka fara ƙerawa a Turkiyya. (Tsohon Hoto) / AP

Ankara ta yi shirin ware kusan dala biliyan biyu ga masana’antun sufurin sama da na sararin samaniyarta cikin shekaru uku masu zuwa, in ji wani daftarin kasafin kuɗin gwamnatin ƙasar na 2027 da bayanan kare kasafin kuɗi.

Kasafin kudin da aka ware wa tsarin sararin samaniya na sufuri na ƙasa ya tsaya a kan dala miliyan $176 ne a wannan shekarar, kuma ya shirya domin ƙaruwa da kashi 181.7 cikin 100 zuwa dala miliyan $495.7 a shekarar 2027 domin ƙarfafa matsayin Turkiyya a fannin a duniya.

Ana san ran kuɗin da za a saka zai ƙara ƙaruwa zuwa dala miliyan $616.9 a shekarar 2028 da kuma dala miliyan $745 a shekarar 2029.

A ƙarƙashin tsarin kashe kuɗin, za a ware kimanin dala miliyan $377.3 ne ga gine-gine da gudanarwa da gyara kayayyakin sufurin sama inda jumullar jarin da za a zuba kan kayayyakin sufurin sama zai kai dala miliyan $581.1 a shekarar 2028 da kuma dala miliyan $596.2 a shekarar 2029 domin iya biyan buƙatar ƙaruwar buƙatar sufurin saman cikin gida.

Ankara na son karɓar baƙuncin matafiya ta filayen jiragen sama miliyan 272 a shekara mai zuwa, ciki har da masu bin filayen jiragen ƙasar daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa ba tare da shiga cikin biranen Turkiyya ba, miliyan 282 a shekarar 2028 da kuma miliyan 291 a shekarar 2029.

Kayayyakin kewayen samaniyar duniya

Kasafin kudin sararin samaniyar da aka faɗaɗa zai tallafa wa Tsarin Sararin Samaniyar Turkiyya da bincike na musamman da gwada kayayyaki da kuma kasuwantar da fasahohi na cikin gida.

Matakin na zuwa ne bayan muhimman ci-gaba da aka samu a fannin cikin ‘yan shekarun nan, ciki har da harba tauraron ɗan Adam na sadarwa na farko na ƙasar, Turksat 6A, da kuma tauraron ɗan Adam na sa ido kan duniya, Imece.

Turkiyya ta kuma kammala tafiya sama ta kimiyya da mutanenta na farko a shekarar 2024, a lokacin da matafiya sararin samaniya Alper Gezeravci da Tuva Cihangir Atasever suka yi gwaji a kewayen duniya.

Birnin kudu maso yammaci na Antalya ya karɓi baƙuncin taron tafiye-tafiyen sararin samaniya (IAC) na 77 daga ranar 5 zuwa 9 na watan Oktoba, gabanin shirye-shiryen tafiya can cikin sararin samaniya zuwa duniyar wata da aka shirya yi a shekara mai zuwa.

Tafiyar ta duniyar wata ta dogara ne kan wani jirgin sararin samaniya da aka ƙera a cikin gida wanda kashi 80 cikin 100 na kayayyakinsa kayayyaki ne da aka samar daga cikin gida da kuma wani tsarin tafiya mai amfani da makamashi daban daban, an kammala haɗa jirgin kuma ana kan gwada shi ne.

A halin yanzu, Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Turkiyya tana ƙara ƙoƙarin samar da wata tashar sararin samaniya a Somalia don tabbatar dama ta kai ta zuwa kewayen duniya.