Ƙungiyar Ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta, wadda ke yaƙi da mayakan Houthi na Yemen, ta bayyana a ranar Lahadi cewa rundunar tsaron sararin samaniyarta ta tare da lalata makamai masu linzami guda huɗu, ciki har da guda biyu masu cin dogon zango da wasu makamai masu linzami biyu masu tafiya ƙasa-ƙasa.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Manjo Janar Turki al-Maliki a cikin sabuwar sanarwar da ya wallafa a shafin X ya bayyana cewa, “Rundunar tsaron sararin samaniya ta tare da lalata makamai masu linzami guda biyu a yankunan Riyadh da kudancin Saudiyya.”
Sai dai Al-Maliki bai yi ƙarin bayani kan daga inda aka harbo makamai masu linzamin ba.
Sanarwar ta zo ne ƙasa da awa guda bayan da ya bayyana cewa rundunar tsaron sararin samaniyar ƙungiyar ta tare da lalata wasu makamai masu linzami guda biyu da mayakan Houthi suka harba zuwa babban birnin Saudiyya wato Riyadh.
Tun da farko a ranar Lahadin, ƙungiyar ta kuma sanar da tare wani makami mai linzami da mayakan Houthi suka harba zuwa yankin Gabashin Saudiyya.
Waɗannan abubuwa na faruwa ne a daidai lokacin da rikicin soji tsakanin ƙungiyar haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya da mayakan Houthi na Yemen ke ci gaba da tsananta, inda mayakan Houthi ke kai hare-hare akai-akai da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa cikin ƙasar Saudiyya.



















