An kai hari kan ayarin motocin fittacen ɗan siyasar adawa a Nijeriya, Peter Obi a jihar Cross River da ke kudancin ƙasar, inda jami'an 'yansanda suka kama wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin, kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Alhamis.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, jim kaɗan bayan Obi da tawagarsa sun kai ziyara fadar Obong na Calabar, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani taro da jam'iyyarsa ta Nigeria Democratic Congress ta shirya.
Rahotannin 'yansanda da kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun ce wasu mahara ɗauke da adduna da sanduna sun yi wa motocin tawagar ruwan duwatsu da wasu abubuwa, lamarin da ya kai ga farfasa gilashin motocin tare da haddasa firgici tsakanin magoya bayansa da 'yankasuwa a yankin.
Rundunar 'yansandan jihar Cross River ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 27 mai suna Victor Edet Yellow Duke, bisa zargin hannu a harin. Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
'Yan siyasa na fuskantar hare-hare
Wannan hari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan makamancin haka da aka kai wa Omoyele Sowore, ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam'iyyar African Action Congress, a Jihar Ekiti.
Jam'iyyun siyasa a Nijeriya na ƙara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda Shugaba Bola Tinubu ke neman wa'adi na biyu a ƙarƙashin Jam'iyyar APC mai mulki.
Wasu fitattun 'yan adawa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Peter Obi, sun gabatar da manufofi daban-daban domin magance matsalar tsaro, matsin tattalin arziki da ƙalubalen shugabanci a ƙasar.
Zaɓen da ake sa ran gudanarwa a watan Janairu mai zuwa zai mayar da hankali kan matsalolin tsaro da dabarun farfaɗo da tattalin arziki, waɗanda za su taka muhimmiyar rawa wajen rinjayar zaɓin masu kaɗa ƙuri'a.



















