| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Isra’ila ta kai hare-hare fiye da 1,000 kan Syria cikin shekara biyu - Ministan Harkokin Waje
Shaibani ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani zama kan tsaron yankin Gabas ta Tsakiya a taron Manama Dialogue na 2026, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Syria (SANA) ya ruwaito.
Isra’ila ta kai hare-hare fiye da 1,000 kan Syria cikin shekara biyu - Ministan Harkokin Waje
Isra’ila ta kai hare-hare fiye da 1,000 kan Syria cikin shekara biyu - Ministan Harkokin Waje

Ministan Harkokin Wajen Syria, Asaad al-Shaibani, ya ce Isra’ila ta kai hare-hare sama da 1,000 a ƙasarsa cikin ƙasa da shekaru biyu, inda ta kashe gomman mutane.

Shaibani ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani zama kan tsaron yankin Gabas ta Tsakiya a taron Manama Dialogue na 2026, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Syria (SANA) ya ruwaito.

“An kai hare-hare sama da 1,000 kan ƙasarmu cikin ƙasa da shekaru biyu, inda aka kashe gomman mutane,” in ji shi.

Ya kuma tambayi yadda za a iya buƙatar Syria ta tsaurara tsaron iyakokinta tare da mayar da dukkan makamai ƙarƙashin ikon gwamnati, alhali ana take haƙƙin mallakar ƙasarta tare da ci gaba da kai mata hare-hare a kullum.

Da yake Allah wadai da hare-haren Isra’ila, Shaibani ya yi kira da a koma kan iyakokin da ake da su kafin ranar 8 ga Disamban 2024, tare da aiwatar da yarjejeniyar dakatar da arangama ta shekarar 1974.

Ya jaddada cewa tuddan Golan da Isra’ila ta mamaye mallakin Syria ne, yana mai cewa ƙudurin kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba 497 shi ne ginshiƙin da ya kamata a bi wajen warware batun.

Tun bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a Syria a ranar 8 ga Disamba, 2024, Isra’ila ta mamaye yankin da aka ware domin zama tsakanin sojojin Syria da Isra’ila bisa yarjejeniyar 1974, tare da kafa sansanonin soji a ciki da wajen yankin.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana matakin na Isra’ila a matsayin saɓa wa yarjejeniyar ta 1974.