| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
’Yansanda sun dakile harin ‘yanta'adda a Zamfara, sun gano gawarwaki fiye da 30
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026.
’Yansanda sun dakile harin ‘yanta'adda a Zamfara, sun gano gawarwaki fiye da 30
’Yansanda sun dakile harin ‘yanta'adda a Zamfara, sun gano gawarwaki fiye da 30

Rundunar ’yansandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta ce jami’anta sun dakile wani yunƙurin harin da ’yan ta’adda suka yi a garin Bukuyum da ke ƙaramar hukumar Bukuyum ta jihar.

Rundunar ta kuma ce ta gano gawarwaki sama da 30 da ake zargin na ’yan ta’addan da aka kashe ne a gonakin da ke kewaye da yankin, bayan arangamar da aka yi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026.

A cewar sanarwar, an fara aikin kakkabe ’yan ta’addan ne ranar 28 ga Oktoba, bayan wani yunƙurin kai hari garin Bukuyum da wasu ’yan bindiga suka yi.

Sanarwar ta ce jami’an ’yan sanda, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron sa-kai na yankin, sun fafata da maharan a wani kazamin musayar wuta, inda suka hana su shiga garin.

Rundunar ta ce gano gawarwakin sama da 30 na nuni da cewa maharan sun yi asarar rayuka masu yawa yayin arangamar. Sai dai ta jaddada cewa har yanzu ba a tantance ainihin adadin waɗanda aka kashe ba.

Ta bayyana cewa ’yan bindiga kan kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu a yayin arangama daga wuraren da aka fafata, lamarin da ke sa ya yi wuya a tabbatar da ainihin adadin waɗanda suka mutu.

’Yan sandan sun ce dakile harin ya hana yiwuwar salwantar rayuka, lalata dukiyoyi da kuma sake raba mazauna yankin da muhallansu.

Rundunar ta ƙara da cewa bayanan farko na tsaro sun nuna cewa ci gaba da matsin lambar jami’an tsaro ya tilasta wa wasu daga cikin ragowar ’yan ta’addan tserewa daga jihar.

Ta kuma tabbatar da aniyarta ta ci gaba da aikin kakkabe ’yanta’addan tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki, domin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara.