| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Kotun Nijeriya ta soke takarar Atiku da tsige ɓangaren David Mark daga shugabancin ADC
Kotun ta ɗauki wannan mataki ne bayan ta amince da ƙarar da Nafiu Bala Gombe, tsohon mataimakin shugaban ADC na ƙasa ya shigar, inda ya ƙalubalanci halaccin shugabancin jam'iyyar da David Mark ke jagoranta.
Kotun Nijeriya ta soke takarar Atiku da tsige ɓangaren David Mark daga shugabancin ADC
Mai ƙarar ya kuma yi zargin cewa yadda aka naɗa waɗannan shugabanni ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC da kuma wasu tanade-tanaden dokar zaɓe.

Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke duk matakan da suka kai ga zaɓen Atiku Abubakar a matsayin ɗantakarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar ADC a babban zaɓen 2027.

Kotun ta kuma soke zaɓen tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, David Mark, da Rauf Aregbesola da sauran wasu mambobin jam'iyyar a matsayin shugabannin ƙasa na ADC.

A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, mai shari'a Peter Lifu ya ce an kuma soke zaɓen dukkan 'yantakarar da jam'iyyar ta gabatar domin shiga zaɓen 2027, saboda sun samu takardun takara ne ƙarƙashin shugabancin jam'iyyar da kotun ta bayyana a matsayin wanda bai dace da doka ba.

Mai shari'a Lifu ya amince da ƙarar da Nafiu Bala Gombe, tsohon mataimakin shugaban ADC na ƙasa ya shigar, inda ya ƙalubalanci halaccin shugabancin jam'iyyar da David Mark ke jagoranta.

Gombe ya yi iƙirarin cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa, Cif Ralph Nwosu, kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya ba shi damar karɓar ragamar shugabancin ADC.

Saboda haka, ya nemi kotun ta soke duk matakan da shugabancin David Mark ya ɗauka, tare da hana Mark, Aregbesola, sakataren jam'iyyar na ƙasa da sauran mambobin kwamitin riƙon ƙwarya gabatar da kansu a matsayin halastattun shugabannin jam'iyyar.

Mai ƙarar ya kuma yi zargin cewa yadda aka naɗa waɗannan shugabanni ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC da kuma wasu tanade-tanaden dokar zaɓe.

Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025 ta shigar da jam'iyyar ADC, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC), David Mark, Rauf Aregbesola da Ralph Nwosu a matsayin waɗanda ake ƙara na farko zuwa na biyar.

A hukuncinsa, mai shari'a Lifu ya amince da buƙatun Gombe tare da ba shi dukkan buƙatun da ya nema.

Sai dai wannan hukunci ba yana nufin an kawo ƙarshen burin Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban ƙasa ba, domin yana da damar ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara kafin zaɓen 2027, bisa tanade-tanaden dokokin da suka dace.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, sakataren jin daɗin jama'a na ADC na ƙasa, Nkemakolam Ukandu, wanda aka shigar cikin ƙarar a matsayin mai ruwa da tsaki, ya ce jam'iyyar za ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.