| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
EFCC ta bankaɗo haramtacciyar matatar mai da ake zargin ’yan China suna gudanarwa a Jihar Ogun
Hukumar EFCC a Nijeriya ta ce jami’anta na ofishin shiyya na biyu da ke Legas ne suka gudanar da aikin a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, bayan tattara bayanan sirri da sa ido kan ayyukan masu sarrafa dattin mai ba bisa ƙa’ida ba.
EFCC ta bankaɗo haramtacciyar matatar mai da ake zargin ’yan China suna gudanarwa a Jihar Ogun
EFCC ta bankado haramtacciyar Matatar Mai da ake zargin ’yan China ne ke gudanarwa a jihar Ogun ta Nijeriya

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Nijeriya Zagon Ƙasa (EFCC) ta bankaɗo wata matatar mai da ake zargin ’yan China suna sarrafa fetur ba bisa ƙa’ida ba a yankin Ogere na Jihar Ogun da ke kudu maso yamacin ƙasar.

Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Talata ta ce jami’anta na ofishin shiyya ta biyu da ke Legas ne suka gano wurin a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, bayan tattara bayanan sirri da sa ido kan ayyukan masu sarrafa man a matatar ba bisa ƙa’ida ba.

Babu kowa a wurin lokacin da jami’an suka isa, amma sun gano ragowar kayayyakin da ake zargin sun rage daga aikin tace mai, da kuma tankunan da aka binne a ƙarƙashin ƙasa waɗanda ake zargin ana amfani da su wajen narkawa da sarrafa man, a cewar sanarwar da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na X.

Masu AlakaTRT Afrika - EFCC ta kama ’yan China 14 da ɗan Nijeriya a masana’antun sarrafa lithium ba bisa ƙa’ida ba a Ogun

Kazalika ta ce tankuna biyu daga cikin waɗanda aka gano suna dauƙe da wasu abubuwa da ake zargin man dizal ne.

Haka kuma binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna haƙo baƙin mai daga Warri a Jihar Delta da kuma Fatakwal a Jihar Ribas, sannan su kai shi matatar da ke Ogere domin sarrafawa.

A cewar EFCC, ana zargin masu gudanar da wurin da amfani da zafi mai tsanani wajen tace sinadaran man, domin samar da dizal da za a sayar a kasuwar Nijeriya.

Jami’an tsaro da ke wurin sun shaida wa EFCC cewa waɗanda ake zargin ’yan China ne, ko da yake ba su bayyana sunayensu ko sunan kamfanin da ke da alaƙa da matatar ba.

Hukumar ta ce jami’anta sun karɓe iko da wurin yayin da ake ci gaba da bincike domin gano mutanen da ke da hannu a lamarin, tare da tabbatar da wadanda suka mallaki wurin da kuma tantance girman ayyukan da ake zargin haramtattu ne.

EFCC ta ƙara da cewa, wannan samamen ya biyo bayan wani aikin da ta gudanar a baya, inda ta rufe wasu masana’antun sarrafa lithium guda huɗu da ake zargin suna aiki ba bisa ƙa’ida ba a yankin.