Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tana tunani a kan gudanar da jarrabawa ga ‘yan ƙasar masu digiri daga ƙasashen ƙetare, musamman digiri daga ƙasashen Afirka, domin daƙile matsalar digirin bogi da kuma kare martabar karatu.
Daraktar da ke sa ido kan ofishin babban sakataren Ma’aikatar Ilimin ƙasar, Dr Folake Olatunji-David, ce ta bayyana wannan shawarar a Abuja a zama na 37 na Kwamitin dindindin na Ƙasa da ke aiki kan tantance shaidar karatu ta ƙetare.
Wata sanarwa da Boriowo Folasade, Daraktar Watsa labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimin ta fitar ranar Litinin ta ambato Dr Olatunji-David tana jaddada cewa bai kamata karatu na ƙasashen ƙetare ya gaza kai matakin da ake iya lamunta ba.

Ta bayyana buƙatar ƙarfafa tantancewa da kuma tabbatar da cewa masu shirin yi wa ƙasa hidima na NYSC sun halarci makarantun da ke ba da shaidun kammala karantunsu.
Dr Olatunji-David ta bayyana cewa Ma’aikatar ta tsara hanya mai sarrafa kanta ta dijital ta tantance tarkardun shaidar karatun ƙetare da na Nijeriya tun daga farkon wannan shekarar, lamarin da ya inganta fayyace gaskiya da inganci da gabatar da aiki.
Kwamitin zai kuma yi nazari game da sa ido kan ‘yan Nijeriya da ke karatu a makarantun Afirka, da amincewa da hukumomi masu sa ido na ƙetare a matsayin wurare masu tushe na iya tabbatar da takardun shaidar karatu da kuma tsara ƙa’idoji na tabbatar da kwatankwacin takardun kammala karatun sakandare.
Sauran batutuwa sun haɗa da biyayya ga manufofin karatun ƙasa daga makarantu masu bin tsarin ƙasashen ƙetare da ke aiki a cikin Nijeriya da kuma tsare-tsaren bayar da wasiƙar rashin ƙi ga makarantun da lamarin ya shafa.
Ma’aikatar ta jaddada jajircewarta ga ƙarfafa tsare-tsaren tantancewa da na sa ido domin tabbatar da takardun shaida na gaskiya daga makarantun da aka yarda da su ne kawai za su samu yarda a hukumance.




















