Hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya ta yi zargin cewa ana samun ƙaruwar ‘yan ƙasashen waje masu ya da zango a ƙasar yayin da suke safarar miyagun ƙwayoyi zuwa wasu sassan duniya.
Hukumar ta bayyana cewa a baya bayan nan an kama ‘yan Afirka ta Kudu uku bisa hannu a safarar heroin da koken da tabar wiwi mai yawa.
Mataimakin Darakta a ɓangaren watsa labarai da ba da shawarwari na NDLEA, Francis Okogun, ne ya bayyana haka a Abuja ranar Alhamis a lokacin hira da manema labarai ta haɗin gwiwa tsakaninsu da hukumomin tsaro da na tattara bayanan sirri.
Ya yi zargi cewa wasu ‘yan ƙasashen ƙetare suna ƙoƙarin wucewa da miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya ta haramtacciyar hanya a madadin ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasashen waje, yayin da wasu ke ƙoƙarin shigar da miyagun ƙwayoyi cikin ƙasar.
Kasancewarta a Yammacin Afirka da yin iyakoki da Benin da Nijar da Chadi da Kamaru, ya sa Nijeriya tana da wani muhimmin wuri na cinikayya da kuma kai komo tsakanin Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Okogun ya ce hukumar tana bincike a kan kamen domin tabbatar da inda aka yi niyyar kai ƙwayoyin da kuma gano ƙungiyoyin da ke da hannu a safarar ƙwayoyin.
“A cikin lokacin da aka yi nazari a kai, an kama mutum uku. Abin da ya sa wannan kamen yake da muhimmanci shi ne ƙwayoyi masu yawa da aka samu a wajen su, ciki har da heroin da koken da tabar wiwi da aka sarrafa wanda aka fi sani da suna Loud.”
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ɗin ita ce wata ‘yar Afirka ta Kudu mai suna, Gebashe Sithandiwe Jessie, wadda aka kama a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Fatakwal a watan Oktoban 2026 bisa zargin ƙoƙarin safarar tabar wiwi da aka sarrafa wadda aka fi sani da suna Thai Loud da ta kai kilogiram 32.74 a ɓoye a cikin kayayyakinta.
Wata ‘yar ƙasar Afirka ta Kudu ɗin kuwa Will Jessica Ann, mai shekara 38, an kama ta ne a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja, ranar 6 ga watan Yulin 2026, da bulo 14 na heroin da nauyinsau ya kai kilogiram 5.75.
Okogun ya ce kamen na da muhimmanci domin yawan miyagun ƙwayoyin da aka ƙwace da kuma alaƙar da ake ganin suna da ita da ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa.
Ya ƙara da cewa hukumar tana gudanar da cikakken bincike domin gano ƙungiyoyin da ke da hannu a safarar miyagun ƙwayoyin.



















