Wata kotu a Kenya ta yanke wa shugaban wata ƙungiyar asiri mai suna Paul Mackenzie hukuncin ɗaurin shekaru 200 a gidan yari a ranar Jumma'a, bisa laifin kisan yara 190 da aka kashe ta hanyar barin su da yunwa, kafin daga bisani aka binne gawawwakinsu a wani daji.
Yaran na daga cikin kusan mutum 500 da ake zargin sun mutu sakamakon ɗaya daga cikin munanan kisan kiyashin da aka aikata a wannan zamani.
Mai Shari’a Diana Kavedza ce ta bayyana hukuncin, inda ta ce an yanke masa shekaru 100 bisa laifin kashe yaran ta hanyar hana su abinci, sannan wasu shekaru 100 bisa laifin kisa kai tsaye.
Masu shigar da ƙara sun bayyana cewa Mackenzie, wanda ya jagoranci wata cocin Kiristanci mai koyar da ilimin ƙarshen duniya a wani daji kusa da gabar tekun Indiya da ke gabashin Kenya, ya umarci mabiyansa da su yi kasance da yunwa har su mutu tare da yaransu, domin su isa Aljanna kafin ƙarshen duniya.
An kuma bayyana cewa waɗanda suka taimaka masa sun riƙa yi wa waɗanda abin ya shafa barazana da duka domin tabbatar da cewa sun bi umarninsa.
An gano gawawwakin mutanen cikin ramuka marasa zurfi a dajin, wasu kuma an jefar da su cikin bandakuna. Wasu daga cikinsu an binne su ne tun suna raye.
Ƙin amincewa da zargin kisan kai
Mackenzie, sanye da riga mai launin toka da wando baƙi, ya yi murmushi yayin da yake shiga wani tanti da aka kafa a wajen kotun da aka gudanar da shari'ar.
Ya musanta zargin kisan kai, yana mai cewa bai tilasta wa waɗanda abin ya shafa su daina cin abinci ba. Sai dai kotun ta yi watsi da wannan kariya tasa.
Lamarin ya girgiza Kenya a watan Afrilun 2023, lokacin da 'yansanda suka fara gano gawawwaki a dajin Shakahola, kusa da garin Malindi da ke gabar teku.
Ko da yake shari'ar ta shafi kisan yara 190 da wani mutum guda, Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Kenya ta bayyana cewa a ƙarshe an gano gawawwaki 448 a cikin dajin.
Haka kuma, ana zargin Mackenzie da bayar da umarnin kashe wasu mutane 52 da aka gano a wani wuri daban, a wani ƙauye mai tazarar kilomita 30 daga dajin. Hakan ya sa adadin mutanen da ake zargin sun mutu ya kai zuwa 500.
Sai dai ya musanta wannan zargi, inda ya ce ba shi da laifi a wata shari'ar da ta shafi waɗannan mutanen.
Yawan mutanen da aka kashe a wannan lamari ya yi kama da kisan kiyashin da wata ƙungiyar asiri mai koyar da ilimin ƙarshen duniya ta yi a Uganda a shekarar 2000, inda aka kashe fiye da mutum 700.
Haka kuma, yana da alaƙa da kisan kiyashin Jonestown na shekarar 1978 a ƙasar Guyana, lokacin da wani shugaban ƙungiyar asiri Ba'amurke ya umarci mabiyansa su sha guba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 900.
Ƙara sanya ido kan ƙungiyoyin addini
Tun daga shekarar 2017 hukumomin Kenya suka fara sanya ido kan Mackenzie, bayan da 'yansanda suka gudanar da bincike a wuraren da yake gudanar da ayyukansa.
A shekarar 2019, hukumomi sun rufe cocinsa da ke Malindi, lamarin da ya sa ya koma gudanar da ayyukansa a dajin Shakahola da ke kusa.
Gano gawawwakin ya haifar da kiraye-kirayen ƙara sanya ido da tsaurara dokokin da ke kula da ƙungiyoyin addini a ƙasar.
A watan Mayun 2023, Shugaban Kenya, William Ruto, ya kafa kwamiti na musamman domin duba dokoki da tsarin kula da ƙungiyoyin addini.
Haka kuma, a shekarar 2024 gwamnati da majalisar dattawan ƙasar sun gabatar da wasu shawarwari daban-daban kan yadda za a ƙarfafa dokokin, sai dai har yanzu ba a mayar da su doka ba.



















