Yayin da Manchester United ke fama da rashin tagomashin ya kai ta gaza cin wasa guda cikin wasanni tara da ta buga a baya-bayan nan, kocin ƙungiyar ya ce ko a jinkinsa.
Da yake magana gabanin wasan da United za ta buga da Roma ta Italiya a gobe 2 ga Nuwamba a gasar Zakarun Turai, Michael Carrick ya ce a daina masa kallon tamkar wanda yake hauka saboda rashin damuwa da barazanar sallamarsa.
Carrick na fuskantar matsin-lamba daga masoya United ganin yadda ƙungiyar ta faɗa rukunin ukun ƙasan teburin Firimiya, waɗanda za su faɗo daga matakin gasar.
United na fuskantar mafi munin hali a gasar Firimiya wanda ba ta samu kanta ciki ba tun shekarun 1980s. Tun Satumba rabonsu da lashe wani wasa a duka gasannin da suke bugawa.
Da yake jaddada cewa hankalinsa kacokan yana kan wasan nasu na gobe, kocin ya ce ba ya jin wani tsoron yiwuwar sallamarsa daga ƙungiyar da ya fara jagoranta daga Mayun shekarar nan.
An ambato Carrick na cewa, “Za ku ce ina hauka ne ganin sakamakon da muke samu, amma ko ma me ya faru, a je a hakan. Kuma za mu ga inda lamura za su kai mu.”
Duk da cewa a yanzu yana da goyon bayan shugabannin ƙungiyar ya amsa cewa ba ba zai “iya hasashen gobe ba, babu wanda ya san gobe. Hankalina yana kan wasanmu na gobe ne.”
Manchester United na fuskantar manyan wasanni biyu a makon nan. Wasa da Roma a gasar Zakarun Turai, da kuma wasa da Aston Villa a gasar Firimiya.
Bayan nan kuma a gasar Firimiya, za su ɓarje gumi da Liverpool. Amma kocin ya ce yana cike da fatan dawowa turbar nasara, saboda yana da cikakken yaƙini kan ƙoƙarin ‘yanwasansa.

















