| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
BAMEX 2026: An fara baje-kolin fasahar tsaro ta ƙasa da ƙasa a Mali
Ana nuna fasahohi na tsaro da kuma tatttaunawa na manyan jami'ai a wurin baje kolin.
BAMEX 2026: An fara baje-kolin fasahar tsaro ta ƙasa da ƙasa a Mali
An ƙaddamar da BAMEX a shekarar 2025 kuma ya fara faɗaɗa, ind aya tara kamfanonin tsaro daga faɗin duniya

An fara taron BAMEX 2026, wanda ya zama ɗaya daga cikin mafi muhimmancin taro kan tsaro a Afirka, a babban birnin ƙasar Mali, inda ake tsammanin nuna fasashohi na tsaro da yawa daga ranar 9 zuwa 13 na watan Nuwamba.

Taron da kamfanin Turkiyya Peak Defence ya tsara, a ƙarƙashin jagorancin Fadar Shugaban ƙasar Mali da Ma’aikatar Tsaro, mai suna Taron Baje-kolin Kayayyakin Tsaro na Bamako na Ƙasa da Ƙasa (BAMEX 2026) wata dama ce ta ƙarfafa tattaunawa na masana’antar tsaro tsakanin kasuwannin Afirka da na ƙetare.

Mataimakin ministan tsaron Turkiyya Bilal Durdalı, da mataimakin shugaba a Ofishin da ke sa ido kan masana’antun tsaro na fadar Shugaban ƙasar Turkiyya Gökhan Ucar da Firaministan Mali Abdoulaye Maiga da ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop da Wakilin Minsitan Tsaron Mali Oumar Diarra suna wajen, tare da manyan wakilai na soji da jami’ai daga fiye da ƙasashen Afirka 40.

Taron mai suna BAMEX da aka fara yi a shekarar da ta gabata inda kamfanonin masana’antar tsaron Turkiyya suka halarta, yana faɗaɗa a wannan shekarar da ƙarin halartar ƙasashen ƙetare.

Baya ga fiye da kamfanoni 20 daga Turkiyya, kamfanonin masana’antar tsaro daga wasu ƙasashen Afirka—ciki har da Sudan da Nijar da Burkina Faso da DR Congo da Uganda tare da masu shiga daga wajen nahiyar kamar Rasha da China da Jamus— suna nuna kayayyakinsu a baje kolin.