| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An kashe mutum 418, an sace 227 a cikin wata biyu a Nijeriya, in ji rundunar 'yansandan ƙasar
Rahoton rundunar 'yansandan Nijeriya ya ce, an kama mutane 1,519 da ake zargi da aikata laifuka, tare da ƙwato bindigogi 191 da alburusai 3,873, sannan ta ƙwace motoci 117 da aka sace ko kuma ake amfani da su wajen aikata laifuka.
An kashe mutum 418, an sace 227 a cikin wata biyu a Nijeriya, in ji rundunar 'yansandan ƙasar
An kashe mutum 418, an sace wasu 227 a cikin wata biyu – 'Yansandan Nijeriya

Rundunar 'yansandan Nijeriya ta bayyana cewa ta samu rahoton hare-haren 'yanbindiga har 168 da ayyukan ta'addanci 51 a sassa daban-daban na ƙasar cikin makonni takwas da suka wuce, kamar yadda rahoton ayyukanta da aka fitar a watan Nuwambar 2026 ya bayyana.

Kazalika rahoton ya ce a cikin watanni biyun an kashe mutane 418 sakamakon hare-haren, yayin da aka samu rahotannin garkuwa da mutane 227 da fashi da makami guda 165, da rikicin ƙungiyoyin asiri 73 da kuma laifukan cin zarafin mata da jinsi 49.

Haka kuma rahoton ya ce, rundunar 'yansandan ta kama mutane 1,519 da ake zargi da aikata laifuka, tare da ƙwato bindigogi 191 da alburusai 3,873, sannan ta ƙwace motoci 117 da aka sace ko kuma ake amfani da su wajen aikata laifuka.

Masu AlakaTRT Afrika - 'Yansanda sun kama mutum 103 da ƙwayoyi da makamai a jihar Borno ta Nijeriya

Jami’an tsaro sun ceto mutane 255 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kawar da wasu 56 da ake zargin ‘yanbindiga ne yayin samamen tsaro a faɗin Nijeriya, in ji rahoton.

A cewar rahoton, rundunar ‘yansandan ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa bayanan sirri da amfani da fasahohin zamani, tare da haɗin gwiwar rundunar soji da sauran hukumomin tsaro, domin yaƙi da ta’addanci da ‘yanbindiga da masu garkuwa da mutane da kuma ƙungiyoyin asiri.

“A tsawon waɗannan watanni biyun, rundunar 'yansandan Nijeriya ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro masu tsauri, bisa bayanan sirri da amfani da fasahohin zamani, tare da haɗin gwiwar rundunar soji da sauran abokan hulɗa a ɓangaren tsaro, domin daƙile ayyukan 'yanta'adda, da 'yanbindiga, da masu garkuwa da mutane da kuma ƙungiyoyin asiri a dukkan sassan ƙasar,” in ji rahoton.

A ƙarin haske da ta yi kan halin da ake ciki na tsaro a Nijeriya, rundunar 'yansandan ta ce, bayanan laifuka daga sassa daban-daban na Nijeriya sun nuna cewa ana sai ido tare da ɗaukar tsauraran matakan tsaro sosai, musaman a yankunan da ke fuskantar barazanar rashin tsaro.

'Yansandan sun danganta nasarorin da aka samu da jajircewa da sadaukarwar jami'ansu, tare da jaddada ƙudurinsu na kare rayuka da dukiyoyin al'umma a faɗin ƙasar.

“Waɗannan nasarori sun zama shaida ta jarumta da sadaukarwa da jajircewar jami'an rundunar 'yansandan Nijeriya, waɗanda ke ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya dora musu na kare rayuka, da al'ummomi da kuma tabbatar da tsaron ƙasarmu, ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar na 'yansanda,” a cewar rahoton.