| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Erdogan da shugaban Nijar sun tattauna batun tsaro da dangantakar kasashen biyu ta wayar tarho
Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya jaddada goyon bayan ƙasarsa ga cikakken ikon Nijar kan yankunanta da kuma tsaron ƙasar, tare da yin alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.
Erdogan da shugaban Nijar sun tattauna batun tsaro da dangantakar kasashen biyu ta wayar tarho
Erdogan da shugaban Nijar sun tattauna batun tsaro da dangantakar kasashen biyu ta wayar tarho

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da takwaransa na Nijar, Abdourahamane Tchiani, sun tattauna ta wayar tarho kan dangantakar Ƙasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi yankin.

Hukumar Sadarwa ta Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya ce ta bayyana hakan.

Masu AlakaShugaba Erdogan ya karbi bakuncin Tiani na Nijar a birnin Ankara na Turkiyya - TRT Afrika - TRT Afrika

A yayin tattaunawar da suka yi a ranar Litinin, Erdogan ya ce za a ci gaba da ƙoƙari da kuma ɗaukar matakan ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu a fannoni daban-daban, kamar yadda hukumar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta wallafa a dandalin sada zumunta na NSosyal.

Haka kuma, Erdogan ya sake tabbatar da goyon bayan Turkiyya ga cikakken ikon Nijar kan yankunanta da tsaron ƙasar, yana mai bayyana shirye-shiryen Ankara na bayar da dukkan taimakon da ya dace domin samar da hanyoyin tattaunawa da ƙarfafa haɗin gwiwar yankin.

Bugu da ƙari, Erdogan ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Tiani da al'ummar Nijar bisa rasuwar mahaifin shugaban ƙasar a makon jiya.

Masu AlakaTRT Afrika - Turkiyya da Nijar sun sanya hannu yarjejeniyoyin hadin kai bayan tattaunawar shugabannin kasashen