Ma’aikatar kiwon lafiyar ƙasar Ghana ta ce ta fara shirin tunkarar Ebola bayan cutar ta ɓulla a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Kenya da Nijeriya.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X, wadda ministan lafiyar ƙasar Kwabena Mintah Akandoh ya sanya wa hannu, ta ce shirin ya zama wajibi ne duba da yadda ake samun kai komon ababen hawa tsakanin Ghana da Kenya da Nijeriya.
“Lamarin da ke faruwa a Kenya na gagarumar barazana ga Ghana domin tafiyar jiragen saman kai-tsaye tsakanin ƙasashen biyu da kuma yawan fasinjoji da ya fi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo,” in ji sanarwar.
“Bugu da ƙari, tabbatar da cutar a Nijeriya ya sake dagula lamari saboda yawan sufuri tsakanin ƙasashen biyu,” in ji ma’aikatar.
Wannan ne ya sa ƙasar za ta ƙarfafa matakan shirya wa ɓullar cutar, in ji ma’aikatar lafiyar.
Ta ce duk da cewa kawo yanzu ba a samu wanda ke ɗauke da cutar a Ghana ba, ƙasar za ta fara ɗaukar matakan shirin rigakafi da inganta sa ido a hanyoyin shiga ƙasar, ciki har da ƙarfafa tantance masu shiga ƙasar.
Kazalika ma’aikatar ta ce za ta ci gaba da tuntuɓar muhimman masu ruwa da tsaki ciki har da Kamfanin filayen jiragen sama na Ghana da hukumar kula da sufurin sama na Ghana da sauransu wajen ƙarfafa shiri da aiki tare.
Har wa yau sanarwar ta ce za a rinƙa horaswa a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Accra da Cibiyar Hana Yaɗuwar Cututtuka ta Ghana domin tantance da kuma inganta shirin tunkarar cutar.

Ɗaya daga cikin matakan da ma’aikatar za ta ɗauka sun haɗa da bin diddigin matafiya daga wuraren da ke da babbar barazanar cutar a iya zamansu a Ghana bisa ƙa’idojin lafiyar jama’a.
Sanarwar ta kuma ce za a ƙarfafa shirin ɗakunan gwaje-gwaje da kuma ƙa’idojin aiki da suka dace tare da wayar da kan ma’aikatan jinya domin su kasance cikin shiri kuma su ɗauki matakan da suka dace kan waɗanda ake zargin suna ɗauke da cutar.
Kazalika ministan lafiyar ƙasar ya ce ma’aikatar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a a filin jiragen saman ƙasar domin sanar da matafiya yadda za a hana yaɗuwar cutar da kuma abin da ya kamata su yi idan suka ga mai alamun cutar.
Wannan ita ce ɓullar cutar Ebola mafi muni a tarihin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo inda fiye da mutum 9,000 suka kamu da cutar yayin da cutar ta kashe fiye da mutum 4,000 tun tsakiyar watan Mayun wannan shekarar 2026.
A ranar 6 ga watan Oktoba ne ƙasar Kenya ta ba da rahoton samun shigowar cutar Ebola ƙasar kuma zuwa ranar 17 ga watan, ƙasar ta ba da rahoton ƙarin mutum shida da suka kamu da cutar ciki har da ma’aikan jinya.
Ita kuma Nijeriya ta ba da rahoton tabbatar da cewa wata da ta shigo ƙasar daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta hanyar Uganda ta kamu da cutar.
Ƙasar Uganda dai ta ce kawo yanzu babu wanda aka tabbatar yana da cutar a cikin ƙasarta.





















