Aƙalla Kiristoci ’yan Orthodox 60 ne aka kashe a wasu hare-hare daban-daban da aka kai a ranakun 20 da 24 ga Oktoba a yankin Oromia na Ethiopia.
Haka kuma, wasu fiye da 20 sun jikkata, yayin da aka ƙona gidaje 20, kamar yadda jami’an cocin suka bayyana a wata sanarwa da suka fitar ranar Litinin.
“Mun samu rahoton da ofishin diocese ya gabatar cikin matuƙar baƙin ciki,” in ji Majalisar Ikilisiyar Mai Tsarki ta Cocin Orthodox ta Ethiopia. Majalisar ta bayyana kashe-kashen a matsayin “zalunci mai tsanani da wahala da aka ƙaƙaba wa ’yan ƙasarmu”.
Cocin ta ce an kashe mutum 14 a ranar 20 ga Oktoba a yankunan Gora Silingo da Angada Kebele, da ke gundumar Merti. An kuma kashe wasu mutum 46 a ranar 24 ga Oktoba a yankunan Tereta, Chole da Birbo, da ke gundumar Shirka.
Dukkan gundumomin biyu suna yankin Arsi ne, a lardin Oromia da ke tsakiyar Ethiopia.
Majalisar Ikilisiyar ta yi Allah wadai da kashe-kashen, tana mai cewa hare-haren sun keta haƙƙin rayuwa da ’yancin yin ibada da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada, tare da yin barazana ga al’adar zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban a Ethiopia.
Ta yi kira ga hukumomin gwamnati da su fito fili su yi Allah wadai da hare-haren, su ƙarfafa kariyar fararen hula, tare da tabbatar da cewa an hukunta waɗanda aka samu da hannu a kashe-kashen.
Cocin ta kuma buƙaci hukumomin tsaro da su ƙara samar da kariya ga al’ummomin da abin ya shafa, tare da ɗaukar matakan da za su hana sake afkuwar irin wannan tashin hankali.
Gwamnatin lardin Oromia ta sha alwashin bin diddigin waɗanda suka aikata kisan.
Rahotannin kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ambato wani jami’in lardin yana zargin wata sabuwar ƙawancen ƙungiyoyin ’yan tawaye, wadda ta haɗa da ƙungiyar Oromo Liberation Army (OLA), da kai hare-haren. Sai dai a baya, OLA ta musanta zarge-zargen kai hare-hare kan fararen hula.
Kashe-kashen na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar tsaro a Oromia, lardi mafi girma a Ethiopia, inda dakarun gwamnati suka shafe shekaru suna fafatawa da ƙungiyoyin ’yan bindiga.
A watan Yuli, Hukumar Kare Haƙƙin Bil Adama ta Ethiopia ta bayar da rahoton cewa an kashe aƙalla fararen hula 432 da mayaƙan yankin huɗu a wasu hare-hare da aka kai a sassa daban-daban na gabashin Arsi tsakanin shekarun 2021 da 2022 zuwa ranar 1 ga Yuni.
Majalisar Ikilisiyar Mai Tsarki ta ce za ta nemi tattaunawa da manyan jami’an gwamnati domin nemo mafita ga matsalar tsaron.
Ta kuma sanar da gudanar da addu’o’i ga waɗanda abin ya shafa a ranar Litinin, tare da umartar cocin Orthodox da gidajen ’yan zuhudu a faɗin duniya da su gudanar da irin waɗannan addu’o’i a ranar Talata.
Cocin ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda aka kashe, tare da yin kira da a ɗauki matakan gaggawa domin tabbatar da cewa mabiyanta za su iya rayuwa da gudanar da ibada ba tare da fargaba ba.











