| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da kisan Sheikh Masussuka, ya bayar da umarnin gudanar da bincike
Wasu ’yan bindiga ne suka kashe mutanen biyu a wani hari da suka kai musu a cikin mota a yammacin ranar Litinin.
Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da kisan Sheikh Masussuka, ya bayar da umarnin gudanar da bincike
Tinubu da Masussuka

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa, Adamu Abubakar, a Dutsin-Ma, Jihar Katsina.

Wasu ’yan bindiga ne suka kashe mutanen biyu a wani hari da suka kai musu a cikin mota a yammacin ranar Litinin.

A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana matuƙar alhini kan labarin kisan, yana mai cewa aikata irin wannan mummunan laifi cin zarafi ne ga ƙimar zaman lafiya da kuma tsarkin rayuwar ɗan’adam.

Masu AlakaTRT Afrika - ’Yanbindiga sun kashe malamin addinin Musulunci a Nijeriya Sheikh Yahya Masussuka - ʼYansanda

Shugaban ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, mabiyansu, da kuma gwamnatin Jihar Katsina da al’ummarta bisa wannan babban rashi.

Shugaba Tinubu ya umarci rundunar ’yan sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gaggauta ƙarfafa binciken da rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta riga ta fara, domin gano waɗanda suka aikata kisan, cafke su tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

Shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan, Ya ba su rahama, sannan Ya ba iyalansu da duk waɗanda suke makokin rasuwarsu haƙurin jure wannan rashi.