| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Rahotanni sun ce majalisar ta amince da tura wani ɓangare na sojojin ƙasar zuwa Nijar don tabbatar da tsaron ayyukan man fetur na kamfanin Sonatrach na Aljeriya da ke aiki a Nijar ɗin.
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Idan aka tura sojojin, wannan mataki zai kasance irinsa na farko tun bayan yaƙin Larabawa da Isra’ila na shekarar 1973.

Majalisar Ƙasa ta Aljeriya, wato majalisar dattijai, ta yi kuri'a a ranar Lahadi don amincewa da kudirin tura wata rundunar soja zuwa Nijar.

An gudanar da kuri'ar ne a wani zama da aka rufe, inda aka kira membobin majalisar su halarta a ranar Alhamis don wani taron gaggawa.

A cewar wani wakilin Anadolu, zaman ya ƙare da raba murya ɗaya na amincewa da shawarar shugaban ƙasa ta tura rundunar soja zuwa Nijar.

Mambobin majalisar sun shaida wa 'yan gidan jarida na cikin gida cewa matakin ya haɗa da "tura wani ɓangare na sojojin ƙasa don tabbatar da tsaron ayyukan mai na kamfanin Sonatrach na Aljeriya a ƙasar makwabta," in ji wakilin.

Irinsa na farko

Ana sa ran majalisar wakilan ƙasar, wadda ita ce ƙaramar majalisar dokokin ƙasar, za ta gudanar da zama a yammacin ranar Lahadi domin kaɗa ƙuri’a kan wannan kudiri.

Sashe na 91 na kundin tsarin mulkin Aljeriya ya tanadi cewa shugaban ƙasa na iya “yanke shawarar tura rundunonin soji zuwa ƙasashen waje bayan samun amincewar kashi biyu bisa uku na mambobin kowace daga cikin majalisun dokokin ƙasar guda biyu”.

Idan aka tura sojojin, wannan mataki zai kasance irinsa na farko tun bayan yaƙin Larabawa da Isra’ila na shekarar 1973.