| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Nijar ta zargi Chadi da haɗa baki da Faransa wajen kai mata hari
Sanarwar da aka karanta ranar Litinin da yamma ta ce harin da aka kai ta yankin Emilulu da ke jihar Agadez ya kashe mutum biyu tare da jikkata wasu mutane.
Nijar ta zargi Chadi da haɗa baki da Faransa wajen kai mata hari
Gwamnatin Nijar ta ce za ta ɗauki matakan da suka dace wajen kare mutane da 'yancin kan ƙasarta

Gwamnatin Nijar ta zargi maƙociyarta Chadi da haɗa baki da Faransa wajen kai hari a ƙasarta.

Wata sanarwar gwamnati da aka karanta a gidan talbijin na gwamnatin Nijar ta ce an kai hari ƙasar Nijar ranar 24 ga watan Oktoba da jirgi maras matuƙi da aka tura daga ƙasar Chadi da tallafin Faransa.

Sanarwar da aka karanta ranar Litinin da yamma ta ce harin da aka kai yankin Emilulu da ke jihar Agadez ya kashe mutum biyu tare da jikkata wasu mutane.

Hukumomi a Yamai sun ce lamarin wata ‘ƙiyayya’ ce da Chadi ke yi wa Nijar ta samar da “muhimman wurare ga sojojin haya” da ke kai hari kan fararen-hula da kayayyaki masu muhimmanci da na makamashi.

Yayin da take Allah wadai da “matakan na tsokana,” gwamnatin Nijar ta yi shelar wasu matakai ciki har da nuna rashin jin daɗi a hukumance ta hanyoyin diflomasiyya sannan ta yi kira ga N’Djamena ta daina nuna mata ƙiyayya.

Gwamnatin ta ce bincike da sojojin ƙasar da hukumomin shari’a suka yi ya tabbatar da daga inda harin ya taho, tana mai ƙarawa da cewa za a gabatar da hujjar ga hukumomi na ƙasa da ƙasa.

Masu AlakaTRT Afrika - Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani ya fara ziyarar aiki a Turkiyya

"Gwamnatin ta yi Allah wadai cikin kalamai mafi ƙarfi da wannan mataki na tsokana wanda ya kasance tsabar keta ‘yancin ƙasa bisa doka ta 2, sakin layi na 4, na takardar kafa Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da kuma ƙa’idojin da suka kafa Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU)," in ji sanarwar.

Gwamnatin ta ce ta ɗora wa Chad alhaƙin "wannan aikin da abin ya haddasa, kuma muna neman kawo ƙarshen dukkan matakai na tsana da kuma biyan diyya ga ta’adin da ta haddasa."

Kazalika gwmanatin ta bayyana matakan da ta ɗauka da kuma bayyana cewa tana da ‘yancin ɗaukar “dukkan matakai da suka dace" wajen kare mutanenta da ‘yancin ƙasarta.

Kawo lokacin da aka rubuta wannan labarin gwamnatin ƙasar Chadi ba ta mayar da martani ba game da zargin.